Isra'ila na ci gaba da kai hari kan fararen hula a Gaza inda take kashe mutane akasarinsu mata da yara. / Hoto: Reuters

1724 GMT — Hezbollah ta yi iƙirarin kai harin makamai masu linzami kan dakarun Isra'ila a kudancin Lebanon

Ƙungiyar Hezbollah ta ƙasar Lebanon ta ce ta harba makamai masu linzami kan dakarun Isra'ila a kudancin ƙasar.

A wata sanarwa da ta fitar, Hezbollah ta ce wani makami mai linzami da ta harba ya faɗa kan sojojin Isra'ila da ke harabar Zebdine sannan ya lalata na'urorin leƙen asiri da ke barikokin soja a Shebaa Farms. Babu bayani game da ko hakan ya yi sanadin kisa ko jikkata wani ko wasu.

1528 GMT — Masar za ta shiga shari’ar Kotun Duniya da Isra’ila

Ƙasar Masar a ranar Lahadi ta bayyana cewa za ta shiga shari’ar kisan ƙare dangi da Afirka ta Kudu ta shigar kan Isra'ila a kotun ƙasa da ƙasa ta ICJ.

A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta fitar, ta ce wannan matakin na zuwa ne “a bisa la'akari da tsananantar hare-haren da Isra'ila ke kai wa kan fararen hula Falasdinawa a Gaza da kuma kai hari kan fararen hula da lalata ababen more rayuwa a cikin tsibiri."

Matakin na Masar na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan Turkiyya ita ma ta sanar da shiga shari’ar kisan ƙre dangin da Afirka ta Kudu ta shigar a gaban Kotun Duniya.

1327 GMT — Sojojin Isra'ila sun kama Falasɗinawa 28 a Gabar Yamma da Kogin Jordan

Rundunar Sojin Isra’ila a ranar Litinin ta kama Falasɗinawa 28 a wasu jerin samamen da ta kai Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye, kamar yadda kungiyoyin kula da fursunoni suka tabbatar.

A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da hukumar kula da fursunonin Falasɗinawa ta fitar ta ce akwai yara da dama daga cikin wadanda ake tsare da su a hare-haren da aka kai a garuruwan Jenin, Jericho, Ramallah, Bethlehem, Hebron, da Qalqilya.

Ana zaman ɗar ɗar a Gabar Yamma da Kogin Jordan tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da kazamin farmakin soji a zirin Gaza, inda kusan mutum 35,000 suka mutu sakamakon harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

0503 GMT — Isra’ila ta kai sabon hari Gaza, likitoci biyu sun rasu

Isra’ila ta sake ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Gaza bayan ta faɗaɗa hare-haren da take kaiwa zuwa Rafah, inda Majalisar Ɗinkin Duniya ke ci gaba da gargaɗi kan cewa kai hari a Rafah da ke cike da mutane zai iya kasancewa babban bala’i.

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Gaza ta ce an kashe likitoci biyu a ranar Lahadi a garin Deir al Balah, inda kafafen watsa labarai suka ruwaito cewa an samu arangama mai muni da luguden wuta ta sama da ƙasa a kusa da Gaza.

Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa Isra’ila ta kai hari a kusa da mashigar Rafah a ranar Asabar, inda hotuna suka nuna yadda hayaƙi ya rinƙa tashi

2258 GMT — Faransa ta yi Allah wadai kan harin Isra’ila a Rafah

Faransa ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai Rafah, kamar yadda ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta bayyama.

“Babu wani wuri mai aminci ga farar hula a Gaza,” kamar yadda ta bayyana, inda ta yi kira ga Isra’ila ta dakatar da kai hare-hare.

Sanarwar ta buƙaci Isra’ila ta koma tattaunawa da Gaza sakamakon “ita ce hanya ɗaya kacal da za a sako waɗanda ake tsare da su da kuma samun dawamammiyar tsagaita wuta.”

2252 GMT — Ɗaliban Yemen sun yi tattaki domin nuna goyon baya ga Gaza

Ɗaliban jami’o’i sun gudanar da zanga-zanga a arewacin Yemen domin nuna goyon bayansu ga Gaza, wadda ke ci gaba da shan baƙar wuya a hannun Isra’ila sakamakon hare-haren da take kai mata.

Ɗaruruwan mutane ne suka taru a arewacin lardin Al-Jawf domin nuna goyon baya ga Gaza a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai mata hari, kamar yadda gidan talabijin na Al-Masirah da ke ƙarƙashin jagorancin Houthi ya nuna.

A yayin da suke ɗauke da tutocin Falasɗinu, masu zanga-zangar sun nuna rashin jin daɗinsu dangane da zaluncin da Isra’ila ke aikatawa. Sun ta faɗin kalamai na ƙin jinin Isra’ila inda suke nuna goyon bayansu ga jama’ar Gaza.

TRT Afrika da abokan hulda