Makiya Musulunci a Denmark sun kona Alkur'ani a gaban ofisoshin jakadancin Turkiyya da Iraki

Makiya Musulunci a Denmark sun kona Alkur'ani a gaban ofisoshin jakadancin Turkiyya da Iraki

Mambobin kungiyar Danske Patrioter mai kyamar Musulunci sun rika rera taken kin jinin Musulmai yayin da 'yan sanda suke ba su kariya.
Kasashen Musulmai sun yi tir da yadda ake ci gaba da kona Alkur'ani a wasu kasashen Turai. / Hoto: AA Archive

Mambobin kungiyar Danske Patrioter mai ikirarin kishin kasar Denmark sun kona Alkur'ani mai tsarki a gaban ofishin jakadancin Turkiyya da ke birnin Copenhagen.

Daga nan kuma suka nufi ofishin jakadancin Iraki da ke birnin inda suka kona wani littafin mai tsarki a gaban ofishin a ranar Asabar.

Mambobin kungiyar mai kyamar Musulunci sun rika rera taken kin jinin Musulmai yayin da 'yan sanda suke ba su kariya.

Labari mai alaka: Sweden ta bari ana ci gaba da kona Alkur'ani

Sun rika nuna yadda suke kona Alkur'anin kai-tsaye a shafukan sada zumunta na intanet.

A watannin baya-bayan nan, irin wadannan kungiyoyi sun kara kaimi wurin kona littafin mai tsarki da kyamar Musulmai, musamman a arewacin Turai, lamarin da ya jawo kakkausar suka daga kasashen Musulmai.

AA