Wata mata Musluma sanya da abaya ke tafiya a kan titin birnin Nantes na Faransa. Hoto: Reuters

Hukumomi a Faransa za su sanya ido kan makarantu sama da 500 don tabbatar da cewa dalibai sun mutunta sabuwar dokar hana sanya abaya a kasar, musamman a yanzu da ake shirye-shiryen komawa makarantu, a cewar Ministan Ilimi na kasar.

A watan jiya ne gwamnatin kasar ta sanar da daukar matakin hana sanya abaya a duk makarantun kasar.

Ta ce yin hakan ya karya ka'idojin ilimin zamani ne wanda tuni ya kai ga haramta sanya lullubi ga mata Musulmai.

Wannan mataki ya yi matukar faranta wa 'yan jam'iyyu da dama rai yayin da ‘yan jam'iyyar masu sassaucin ra'ayi ke cewa hakan cin-fuska ne da kuma take 'yancin walwalar mata Musulmai.

"A halin yanzu akwai makarantu 513 da za mu mai da hankali a kansu don tabbatar da cewa sun mutunta wannan mataki da aka dauka musamman a daidai lokacin da ake shirye-shiryen soma sabon zangon karatu na wannan shekara,"a cewar Ministan Ilimi Gabriel Attal yayin da yake zanta wa da gidan rediyon RTL a ranar Litinin.

Ministan ya ce tuni aka gudanar da aikin bincike kan makarantun da za su iya ba da matsala kan wannan doka, inda ya kara da cewa za a sanya kwararrun da za su sa ido kan makarantun.

Akwai kusan makarantu 45,000 a Faransa, yayin da yara miliyan 12 ke komawa karatu a ranar Litinin.

Jam'iyyar masu sassaucin ra'ayi ta zargi gwamnatin Shugaba Emmanuel Macron mai tsattsauran ra'ayi da kokarin komawa zuwa jam'iyyar National Rally ta Marine Le Pen .

Ko da yake Attal ya ce yana adawa da sanya dokar hana iyaye sanya tufafi da ke alaka da muhimmaci ga wani addini a lokacin da suke raka 'ya'yansu zuwa makaranta.

"Akwai bambanci tsakanin abin da ke faruwa a makaranta da kuma abin da ke faruwa a wajen makaranta, abin da ya dame ni shi ne abin da ke faruwa a makaranta," in ji shi.

Wasu jiga-jigan masu fada a ji a bangaren jam'iyya masu tsaurin ra'ayi da su yi kira ga gwamnati da ta sanya doka ga yara kan suna sanya tufafin da aka ware wa dukkan makarantun gwamnati a duk kasar, kuma Attal ya ce zai fitar da sanarwa kan aikin gwaji lokacin kaka.

"Ba ni da tabbaci kan cewa hakan zai samar da mafita ga matsalolin ko wacce makaranta. Amma ina ganin yana da kyau a yi gwaji akan tasirinsa," in ji shi.

A watan Maris na shekarar 2014 ne aka gabatar da wata doka kan haramta “sanya wasu alamomi ko sutura da dalibai ke alakanta su da addini” a makarantu.

Abubuwan sun hada da manyan tambarin kuros da hular Kippas ta Yahudawa da kuma sanya mayafi na Musulmai.

TRT World