Majalisar tsaron Isra'ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, kamar yadda wata kafar yaɗa labarai ta cikin gida Channe 12 ta rawaito.
Ana sa ran yarjejeniyar za ta fara aiki daga ranar Laraba, kamar yadda rahoton ya bayyana a ranar Talata.
A bangre ɗaya kuma, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya ce a shirye yake ya yi aiki da yarjejeniyar ta tsagaita wuta a Lebanon, kuma zai “mayar da martani da ƙarfi idan Hezbollah ta saɓa yarjejeniyar.”
A wani jawabi da ya gabatar ta gidan talabijin, Netanyahu ya ce zai gabatar wa majalisar ministocinsa cikakken bayanin yarjejeniyar nan gaba a yau, bayan taƙaitacciyar majalisar tsaro ta amince da ita.
“Za mu aiwatar da yarjejeniyar, sannan za mu mayar da martani da ƙarfi idan aka saɓa ta. Za mu ci gaba da samun nasara tare,” a cewarsa.
Ya ƙara da cewa akwai dalilai uku da suka sa aka amince da yarjejeniyar – mayar da hankali kan Iran, da ƙara tara makamai da suka yi ƙasa da kuma bai wa sojoji dama su huta, sannan daga ƙarshe kuma a keɓe ƙungiyar gwagwarmaya ta Hamas.
'Abokan gana na Isra’ila ba su san ya kamata ba'
A wani ɓangaren kuma, a cikin wata sanarwa a ranar Talata, Firaministan Lebanon Najib Mikati ya buƙaci ƙasashen duniya “su ɗauki mataki nan take” don hana hare-haren Isra’ila, sannan “a aiwatar da tsagaita wuta nan take”.
Mikati ya ce irin hare-haren da Isra’ila ta kai Beirut ranar Talata “sun tabbatar da cewa abokan gaba na Isra’ila ba sa martaba kowace irin doka sannan ba su san ya kamata ba”.
“Muna kiran ƙasahen duniya su ɗauki mataki nan take don tsayar da miyagun hare-hare, sannan a tsagaita wuta nan take,” kamar yadda ya faɗa a wata sanarwa, wacce aka fitar gabanin Isra’ila ta ki hari tsakiyar yankin kasuwanci na Hamra.