'Yan majalisa 204 a Koriya ta Kudu suka amince a tsige shugaban. / Hoto: AP

Majalisar Dokokin Koriya ta Kudu ta kaɗa ƙuri'a inda ta tsige Shugaban ƙasar Yoon Suk Yeol saboda ayyana dokar ta-baci da ya yi na tsawon lokaci a wannan watan.

Majalisar dokokin ta amince da hakan ne bayan an jefa ƙuri'a a ranar Asabar inda sakamakon ya kasance na ƙuri'u 204-85.

Za a dakatar da ikon Shugaba Yoon Suk Yeol da ayyukansa bayan an kai masa kwafin takarda kan tsige shi da kuma Kotun Tsarin Mulki ta ƙasar.

Kotun dai tana da kwanaki 180 don tantance ko za ta kori Yoon a matsayin shugaban kasa ko kuma ta maido da ikonsa. Idan aka kore shi daga ofis, dole ne a gudanar da zaben kasa don zaben wanda zai gaje shi a cikin kwanaki 60.

Idan har ta goyi bayan tsige shi, Yoon zai zama shugaban kasa na biyu a tarihin Koriya ta Kudu da aka samu nasarar tsige shi.

Firayim Minista Han Duck-soo - a yanzu shugaban rikon kwarya na kasar - ya shaida wa manema labarai cewa "zan ba da dukkan karfina da kokarina don tabbatar da zaman lafiya".

Ana bukatar kuri’u dari biyu domin tsigewar, kuma ‘yan majalisar adawa sun bukaci akalla ‘yan majalisar wakilai takwas daga jam’iyyar PPP masu ra’ayin rikau ta Yoon su sauya sheka.

TRT World