#LOE11 : Israel and Gaza at war after Hamas launches surprise attack / Photo: AFP

1519 GMT — Hare-haren Isra'ila ya raba kashi 70 cikin 100 na al'ummar Gaza da muhallansu: Falasdinu

Aƙalla Falasɗinawa 6,546 aka kashe a hare-haren Isra'ila inda kashi 70 cikin 100 na al'ummar Gaza kuma suka rabu da muhallansu a cikin mummunan yanayi, kamar yadda ofishin watsa labarai na gwamnatin yankin da aka yi wa ƙawanya suka faɗa.

“An raba Falasɗinawa kusa miliyan 1.4 da muhallansu," a cewra mai magana da yawun ofishin watsa labaran a Gaza, Salama Maarouf.

Ya ce fararen hular da suka rasa muhallan nasu a yanzu suna samun mafaka a wurare 223 ciki har da asibitoci da makarantu da coci-coci da kuma cibiyoyin lafiya.

"Iyalan Falasɗinawan da suka rasa muhallansu suna fama da matsalar rashin abubuwan buƙatar rayuwa a yayin da Isra'ila ke ci gaba da yaƙi da Gaza," kamar yadda Maarouf ya ƙara da cewa.

1257 GMT — Gwamnatin Libiya ta yi kira da a daina fitar da fetur zuwa kasashen da ke goyon bayan Isra'ila

Majalisar dokokin gwamnatin Libiya ta yi kira ga kasashe masu fitar da man fetur da su daina fitar da man zuwa ga kasashen da ke goyon bayan Isra'ila a yakin da take yi da Gaza.

"Muna son gwamnati ta dakatar da fitar da fetur da gas ga ƙasashen da ke goyon bayan Isra'ila idan har ba ta daina kisan kiyashin da take yi a Gaza ba," a cewar mai magana da yawun majalisar Abdullah Belihaq, a wata sanarwa da ya fitar.

Majalisar dokokin wacce ke Gabashin Libiya ta kuma yi kira ga jakadun ƙasashen da ke goyon bayan "munanan ayyukan" Isra'ila a Gaza da su bar ƙasar ba tare da ɓata lokaci ba.

"Majalidar dokokin ta yi tir da goyon bayan laifukan Isra'ila a Gaza da Amurka da Birtaniya da Faransa da Italiya ke yi," a cewar sanarwar.

Ta bayyana cewa rikicin na Gaza "kisan ƙare dangi ne da Amurka da Ƙasashen Yamma ke jagoranta a kan mutanen da ba su da makamai da kuma yi wa mutane ƙawanya."

1045 GMT Turkiyya na jin takaicin yadda MDD ta gaza yin komai a kan kisan yara da ake ci gaba da yi a Gaza - Erdogan

Turkiyya na jin takaici matuƙa kan rashin kataɓus din da Majalisar Dinkin Duniya da dauke kai daga kisan zalincin da ake yi wa yara, a cewar shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

Shirun da masu adawa da Rasha ke yi a yakinta da Ukraine, a kan kisan kiyashin da ake yi a Gaza shi ne mafi ƙololuwar munafunci," ya ƙara da cewa.

Ya kuma ce ya kamata dukkannin bangarorin da ke fada da juna a yakin Falasdinu da Isra'ila su tsagaita wuta ba tare da ɓata lokaci ba.

Erdogan ya ce ya soke shirinsa na ziyartar Isra'ila saboda "rashin tausayin da take nunawa" a yakinta da Gaza.

"Muna da shirin zuwa Isra'ila, amma mun soke shi, ba za mu je ba," Erdogan ya shaida wa 'yan majalisar dokoki na jam'iyyarsa.

0951 GMT — Sojoji takwas sun mutu sakamakon harin Isra'ila a kudancin Syria

Hare-haren da Isra'ila ta kai kudancin Syria a safiyar Laraba ya yi sanadin mutuwar sojoji takwas, kamar yadda kafar watsa labarai ta kasar ta bayyana.

Isra'ila ta ce ta mayar da martani ne kan makamin roka da aka harba mata a baya.

Ci gaba da musayar wuta da harba rokoki tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbollah ta Lebanon ya kara saka fargaba kan cewa akwai yiwuwar a kara samun wani sabon fagen yakin.

0855 GMT — Adadin Falasdinawan da aka kashe a Gabar Yamma da Kogin Jordan ya kai 103

Adadin Falasdinawan da aka kashe a Gabar Yamma da Kogin Jordan tun bayan soma yaki a tsakanin Isra'ila da Falasdinu ya kai 103, ciki har da fursunonin Isra'ila biyu, kamar yadda kididdigar da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ta nuna.

Ma'ikatar Lafiya a ranar Laraba ta fitar da wata sanarwa wadda ta ce "Falasdinawa hudu aka kashe a safiyar nan sakamakon harbin bindiga da kuma rokoki, da kuma wasu uku da aka kashe a Jenin sai kuma daya a Qalqilya.

Sojojin na Isra'ila sun shiga gida-gida a Qalqilya domin gudanar da bincike, inda suka yi arangama tsakaninsu da gomman Falasdinawa.

Sojojin sun harba harsasai na gaske da kuma na roba a lokacin arangamar, kamar yadda wani wanda ya shaida lamarin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

AA
AFP
AP