Laifukan yaki da sojojin Myanmar ke aikatawa wadanda suka hada da harin bama-bamai kan fararen-hula, ''na kara yawa tare da kazanta,'' a cewar sabon rahoton da wata tawagar masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya ta fitar.
A rahoton da kungiyar Independent Investigative Mechanism for Myanmar (IIMM) ta wallafa a ranar Talata, wanda aka yi daga Yulin 2022 zuwa Yunin 2023, ya ce akwai “kwararan shaidu da suka nuna yadda sojojin Myanmar da mayakan sa-kai suka aikata laifukan yaki iri daban-daban wadanda ke karuwa ba kakkautawa."
Laifukan sun hada da yawan kai hare-hare kan fararen-hula ta hanyar amfani da bama-bamai da kona gidaje da gine-ginen al'umma, wanda a wasu lokuta kan kai ga lalata kauyukan baki daya.
Rahoton ya kuma ba da misali kan "kisan fararen-hula ko mayakan da ake tsare da su a yayin kai hare-haren".
“Shaidun da muka samu sun nuna yadda ake samun karuwar laifukan yaki da cin zarafin bil adama a kasar, tare da yawn kai hare-hare a kan fararen-hula, kuma muna tattara hujjojin da kotu za ta yi amfani da su wajen hukunta wadanda suka aikata irin wannan laifin,” in ji Nicholas Koumjian, shugaban kungiyar IMM.
Sojoji sun musanta aikata ta'asa
Tun bayan karbe mulkin Myanmar da rundunar sojin kasar ta yi shekaru biyu da suka gabata, kasar ta fada cikin rudani, yanayin da ya haifar da fafatawa tsakanin ‘yan adawa da sojojin kasar,
Hakan ya kai ga murkushe fararen-hula da dama, lamarin da ya sa kasashen Yammacin Turai suka sake kakaba wa kasar takunkumai.
Kokarin jin ta bakin kakakin gwamnatin sojin Myanmar kan binciken da Majalisar Dinkin Duniyar ta gudanar ya ci tura.
A baya dai gwamnatin mulkin sojin kasar ta musanta cewa an tafka ta'asa, tana mai cewa tana aikin kakkabe 'yan ta'adda.