Rikici a Sudan da kuma mumunan yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza sun sanya adadin 'yan gudun hijira a duniya ya kai mutum miliyan 75.9 ya zuwa karshen shekarar 2023, a cewar wani rahoto da wata kungiya mai zaman kanta ta fitar.
Cibiyar wadda ke sa ido kan mutanen da ke neman mafaka a ranar Talata ta bayyana cewa adadin ya haura wani mataki a karshen shekara, bisa la'akari ƙarin da aka samu na adadin mutanen da suka rasa matsugunansu a tsakanin iyakokinsu da kashi 50 cikin 100i a cikin shekaru biyar da suka gabata.
Adadin ya ƙaru daga mutum miliyan 71.1 a karshen 2022.
'Yan gudun hijira su ne mutanen suka ƙaura zuwa kasashen waje, yayin da masu neman mafaka kuma suka kasance wadanda yaƙi ko wani tashin hankali ya tilasta musu barin matsugunansu.
A rahotonta na shekara-shekara kan mutanen da suka rasa matugunansu, ƙungiyar IDMC ta ce mutum miliyan 68.3 ne a fadin duniya suka rasa matsugunansu sakamakon yaƙi da tashe-tashen hankula, yayin da mutum miliyan 7.7 suka rasa muhallansu sakamakon bala'o'i da iftila'i.
A cikin shekara da suka gabata, yawan 'yan gudun hijira sakamakon yaƙe-yaƙe ya ƙru da mutum miliyan 22.6, inda aka fi samun ƙaruwar a cikin shekarar 2022 da 2023.
Sudan ita ce ta fi yawan mutanen da suka rabu da muhallansu inda take da miliyan 9.1 a karan-kanta ita kaɗai tun daga shekarar 2008, kamar yadda rahoton ya faɗa. Kusan rabin 'yan gudun hijirar da ake da su a duniya 'yan yankin kudu da hamadar saharar Afirka ne.
"A cikin shekaru biyu da suka gabata, mun ga sabbin matakan da suka fi tayar da hankali na mutanen da ke tserewa daga gidajensu saboda rikici da tashin hankali, har ma a yankunan da al'amuran ke ci gaba," in ji daraktan IDMC Alexandra Bilak.
"Rikici, da ɓarnar da al'amuran suka jawom suna hana miliyoyin mutane sake gina rayuwarsu, sau da yawa har tsawon shekaru."
'Gaza ɗaukar mataki'
Har ila yau, ƙungiyar ta ce tana lura da adadin ƙaura daga cikin gida: kowane sabon motsi na tilasta mutum fita daga cikin iyakokinsa. Ana iya raba mutane da matsugunansu sau da yawa.
A bara mutum miliyan 46.9 ne aka tursasa wa barin muhallansu - mutum miliyan 20.5 daga cikinsu an tilasta musu yin ƙaurar ne a cikin ƙasashensu sakamakon rikice-rikice, sai kuma mutum miliyan 26.4 da bala'o'i suka tarwatsa su.
Yaƙin Sudan da na Jamhuriyar Dimokraɗiyar Congo da yankunan Falasɗinu su ne suke da kashi biyu cikin uku na mutanen da aka raba da muhallansu a shekarar 2023.
A Gaza, Falasɗinawa mutum 1.7 aka raba da muhallansu da sa su yin gudun hijira a cikin ƙasarsu zuwa ƙarshen 2023, inda aka sake samun wasu mutum miliyan 3.4 da aka sake tarwatsa su a baya-baya nan. Mummunan yaƙin da ake yi a Gazan ya fara nr tun watan Oktoban bara.
A baki ɗaya shekarar 2023, mutum miliyan shida aka tilasta wa yin ƙaura sakamakon rikicin Sudan - fiye da yawan da aka samu a shekara 14 da suka gabata.
Lamarin shi ne na ƙaura ta biyu mafi yawa da aka tilasta wa mutane yi a cikin shekara guda bayan Ukraine mai mutum miliyan 16.7 a shekarar 2022.
Hukumar Kula da 'Yan gudun Hijira ta Norway ce ta samar da ƙungiyar IDMC a shekarar 1998.
"Ba mu taba samun adadin mutane da yawa da aka tilasta musu barin gidajensu da al'ummominsu ba kamar wannan. Wannan lamari ne mai muni da ke nuna gazawar kasa magance rikice-rikice da samar da zaman lafiya," in ji shugaban NRC Jan Egeland.
"Ba za a zuba ido kan ƙin ɗaukar mataki da ba da taimakon da ke sa miliyoyin mutane ke fama da wannan matsala ba."