Sojojin Isra'ila sun harba wa Falasdinawa barkonon-tsohuwa yayin da suke jira a saki fursunoni. / Hoto: AA

1640 GMT Qatar ta ce an saki 'yan Isra'ila 13, 'yan Thailand 10 da dan Philippine 1

Kasar Qatar da ke shiga tsakanin Isra'ila da Falasdinawa ta ce Hamas ta saki 'yan Isra'ila 13, ciki har da masu rike da fasfo na kasashe biyu da 'yan Thailand 10 da dan Philippine 1.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Qatar ya tabbatar da sakin “mata da kananan yara 39” daga gidajen yarin Isra'ila.

1400 — Hamas ta mika 'yan Isra'ila 13 da 'yan Thailand 12 da ta yi garkuwa da su ga Red Cross

Kungiyar Hamas mai fafutukar kare hakkin Falasdinawa ta mika 'yan Isra'ila 13 da ta yi garkuwa da su ga kungiyar Red Cross a yarjejeniyar musayar fursunoni.

"Awa daya da ta wuce, an mika fursunonin ga Red Cross wadda za ta dauke su zuwa Masar kuma daga nan Isra'ila za ta karbe su," a cewar wata majiya da kamfanin dillancin labarai na AFP ya yi hira da ita. Kazalika wata majiyar ta daban ta battabar sa wannan lamari.

Haka kuma an mika 'yan kasar Thailanda 12 da su ma suke cikin wadanda aka yi garkuwa da su

Babu wani bayani game da Falasdinawa da aka ce Isra'ila za ta saka daga gidan yari a yarjejeniyar musayar fursunoni da aka kulla.

1041 GMT — Dakarun Isra'ila sun harbe wasu Falasdinawa

Dakarun Isra'ila sun harbe wasu Falasdinawa biyu sannan suka jikkata mutum 11 a yayin da suka nufi arewacin Gaza duk da gargadin da Isra'ila ta yi na kada su yi hakan.

Wani dan jaridar kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ga gawawwakin mutanen biyu da kuma wadanda suka jikkata a yayin da aka kai su asibitin Deir al Balah da ke kudancin Gaza. An harbi mutanen da suka jikkata ne a kafafunsu.

An ga daruruwan Falasdinawa suna kokarin tafiya arewacin Gaza tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwana hudu ta soma aiki.

Ganau sun ce dakarun Isra'ila suna bude wuta a kan mutanen da suka yi kokarin tafiya arewacin Gaza daga kudanci.

0746 GMT — Sojojin Isra'ila na ci gaba da kama mutane a Gabar Yammacin Kogin Jordan duk da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Sojojin Isra'ila na ci gaba da kama mutane tare da kai samame a Yammacin Kogin Jordan duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla tsakaninsu da Hamas a Gaza wacce ta soma aiki da sanyin safiya.

A cewar wani mai aiko da rahotanni ga kamfanin dillancin labarai na Anadolu da ke yankin, rundunar sojin Isra'ila ta kai samame a birane da garuruwa da dama a Gabar Yammacin Kogin Jordan inda ta kama Falasdinawa da yawa.

A gefe guda, wasu majiyoyi na hukumomin lafiyar Falasdinawa sun shaida wa Anadolu cewa dakarun Isra'ila sun jikkata akalla Bafalasdine guda loacin da suka kai hari a Tsohon Birni da ke Birnin Nablus.

Kazalika ganau sun ce dakarun Isra'ila sun tsare Falasdinawa biyu a samamen da suka kai Nablus. Dakarun Isra'ila sun kona motoci biyu na Falasdinawa kafin su janye daga yankin.

Isra'ila ta gargadi dubban Falasdinawa da suka samu mafaka a kudancin Gaza da kada su yi yunkurin komawa gidajensu a arewaci. / Hoto: AA

0016 GMT — Shugaban Cuba ya shiga zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa

Shugaba Miguel Diaz-Canel na Cuba ya jagoranci gagarumar zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a yayin da Isra'ila ke ci gaba da yin luguden wuta a Gaza.

Masu gangamin sun rika daga tutocin Falasdinu inda suka caccaki Amurka bosa goyon bayan da take bai wa Isra'ila.

Ma'aikatar Cikin Gida ta kasar ta wallafa sako a shafin X cewa mutum sama da 100,000 sun shiga zanga-zangar.

Shugaban Cuba Miguel Diaz-Canel ya shiga zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa./Hoto: Reuters

0500 GMT Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas ta soma aiki

Yarjejeniyar kwana hudu game da yakin da Isra'ila take yi a Gaza ta soma aiki inda za a yi musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu, a wani mataki na farko na samun sauki tun bayan yakin da ya barke makonni bakwai da suka gabata.

Bayan an dade ana tattaunawa kan tsagaita wuta, yarjejeniyar ta soma aiki da misalin karfe 7 na safe a agogon yankin wato karfe 5 a agogon GMT, inda aka ji saukin rugugin bindigogi tun bayan harin ba-zata da Hamas ta kai wa Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.

Bayan tsagaita wutar, za a saki kashin farko na fursunoni 13 da ake tsare da su a Gaza, da kuma wasu fursunoni Falasdinawa da ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila, a cewar kasar Qatar wadda ita ce take shiga tsakani.

Wannan tsagaita wuta za ta kawo sauki ga mutum fiye da miliyan biyu da ke Gaza, wadanda suka yi ta fuskantar hare-haren Isra'ila, lamarin da ya kashe fiye da mutum 14,500 da raba dubbai daga muhallansu.

Hamas ta tabbatar da cewa za ta tsagaita wuta da misalin karfe 7 na safe lamarin da zai bayar da amar shigar da kayan agaji./ Hoto: Reuters

0420 GMT — Isra'ila ta kai hari wata makarantar MDD, ta kashe mutum 300 da jikkata 100

Akalla mutum 30 sun mutu sannan sama da mutum 100 sun jikkata sakamakon wani hari da Isra'ila ta kai a wata makaranta da Majalisar Dinkin Duniya ke gudanarwa a arewacin Gaza, a cewar kungiyar Hamas mai fafutukar kare hakkin Falasdinawa.

An kai harin ne a Makarantar Abu Hussein wacce hukumar UNRWA ke gudanarwa a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia, a cewar Hamas.

Rundunar sojin Isra'ila ba ta ce komai kan wannan batu ba.

Kawo yanzu Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 14,854, ciki har da kananan yara 6,150 da mata 4,000, a cewar hukumomin yankin./Hoto:AA

0400 GMT — Isra'ila ta kai harin bama-bamai a Asibitin Indonesia da ke Gaza

Dakarun Isra'ila sun kai harin bama-bamai a Asibitin Indonesia da ke arewacin Gaza inda suka lalata inijinin da ke ba shi wutar lantarki, a cewar Ma'aikayar Kiwon Lafiya ta yankin.

"An yi luguden wuta a kan injinin samar da hasken lantarki da kuma babban ginin asibitin," a cewar kakakin ma'aikatar Ashraf al Qudra a wata takaitacciyar sanarwar da ya fitar.

"Rayuwar majinyata 200 da ma'aikatan asibitin na cikin hatsari a yayin da ake ci gaba da kawo hari," in ji shi.

Isra'ila ta ka harin ne gabanin shigar lokacin tsagaita wuta tsakaninta da Hamas ranar Juma'a da misalin karfe 7 na safe a agogon kasar wato karfe 5 a agogon GMT.

Hare-haren da Isra'ila ta kaddamar a Gaza tun 7 ga watan Oktoba sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 14,854, ciki har da kananan yara 6,150 da mata 4,000, a cewar hukumomin yankin.

A nata bangaren, Isra'ila ta ce an kashe 'yan kasarta 1,200.

AA
AFP
Reuters
TRT World