"Amma mun kuduri aniyar ci gaba da yakin bayan dakatawa, domin cimma burin kawar da Hamas. Ba zan yi kasa a gwiwa ba," in ji Netanyahu. / Photo: AA Archive

1450 GMT — Isra'ila ba za ta yarda da yarjejeniyar da za ta kawo ƙarshen yaƙin Gaza ba — Netanyahu

An shiga cikin shakku kan yuwuwar shawarar da Amurka ke mara wa baya ta kawo karshen hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza na tsawon watanni 8 bayan Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce zai amince da wani ɓangare ne kawai na yarjejeniyar tsagaita wuta da za ta kawo karshen yaƙin ba gaba ɗayanta ba, kalaman da suka haifar da hatsaniya daga iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a Gaza.

A wata hira da aka watsa a gidan talabijin na Channel 14 na Isra'ila mai ra'ayin mazan jiya da take goyon bayan Netanyahu, shugaban na Isra'ila ya ce "a shirye yake don aiwatar da wani bangare na yarjejeniyar - wannan ba wani sirri ba ne - wanda zai dawo mana da wasu daga cikin mutanen," yana mai nuni da batun kimanin mutane 120 da ake garkuwa da su a Gaza.

"Amma mun kuduri aniyar ci gaba da yakin bayan dakatawa, domin cimma burin kawar da Hamas. Ba zan yi kasa a gwiwa ba."

Kalaman Netanyahu sun sha bamban da bayanin yarjejeniyar da shugaban Amurka Joe Biden ya yi a karshen watan da ya gabata, wanda ya tsara shirin a matsayin na Isra'ila wanda wasu a Isra'ila ke kira "yarjejeniyar Netanyahu."

Shirin mai matakai uku zai sa a sako sauran mutanen da aka yi garkuwa da su a madadin daruruwan Falasdinawa da Isra'ila ke tsare da su.

Hamas ta dage cewa ba za ta saki sauran mutanen da take garkuwa da su ba har sai an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin da kuma janye dakarun Isra'ila baki ɗaya daga Gaza. A lokacin da Biden ya sanar da sabuwar yarjejeniyar a watan da ya gabata, ya ce ya haɗa dukkan buƙatun a ciki.

0826 GMT — Isra'ila ta kashe daraktan sashen kula da lafiyar gaggawa na Gaza

Ma'aikatar kieon lafiya ta Gaza ta ce Isra'ila ta kashe daraktan sashen kula da lafiyar gaggawa na asibitin Gaza.

A wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta tabbatar da kashe Hani Al Jafrawi a harin da jirin yaƙin Isra'ila ya kai.

Sanarwar ta ƙara da cewa “ma'aikatan lafiya na ci gaba da bayar da agajin jinƙai na kwashe mutanen da suka jikkata da waɗanda suka mutu babu dare babu rana, duk da hare-haren da Isra'ila take ci gaba da kai wa".

0545 GMT —Yara sama da 20,000 sun ɓata sakamakon yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza

Dubban ƙananan yara Falasɗinawa sun ɓata, sannan ɓaraguzai sun danne wasu, kana dakarun Isra'ila suna tsare da wasu, yayin da kuma iyalai suka binne wasu daga suka mutu a kaburburan da ba a yi wa alama ba, a cewar wani sabon rahoto na ƙungiyar agaji ta Save the Children.

Tawagar ƙungiyar da ke sanya idanu kan yaran da aka raba da muhallansu ta ce hare-haren baya bayan nan da Isra'ila ta ƙaddamar a Rafah sun raba ƙarin yara da muhallansu sannan sun jefa dangi da al'ummomin da suka fito cikin ƙarin bala'i.

Yana da matuƙar wahala a tattara bayanai a yanayin da ake ciki a Gaza, amma an yi amannar cewa an raba yara fiye da 17,000 da iyayensu sannan akwai yiwuwar yara aƙalla 4,000 na binne a cikin ɓaraguzan gine-gine bayan an yi luguden wuta a gidajensu, kana adadin da ba a tantance ba na yara na binne a kabirburan da ba a yi wa lamba ba," in ji ƙungiyar da ke Birtaniya.

"Kazalika an ɓatar da wasu da ƙarfin tsiya, cikinsu har da waɗanda aka tsare da kuma waɗanda aka tilasta wa ficewa daga Gaza kuma iyayensu ba su san inda suke ba a yayin da ake zargin cewa ana azabtar da su."

Kazalika an ɓatar da wasu yaran da ƙarfin tsiya, cikinsu har da waɗanda aka tsare da kuma waɗanda aka tilasta wa ficewa daga Gaza kuma iyayensu ba su san inda suke ba a yayin da ake zargin cewa ana azabtar da su, in ji Save the Children./ Hoto: AA

0120 GMT — Isra'ila ta shirya gwabza yaƙi daban-daban — Netanyahu

Isra'ila tana shirin sauya lamura a kan iyakarsa da Lebanon amma tana fatan ba za ta buƙaci yin hakan ba, in ji Firaminista Benjamin Netanyahu, yayin da yake magana game da fafatawar da sojojinsu suke yi da ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon.

Da yake hira da gidan talbijin na Channel 14 game da yiwuwar tsunduma yaƙi gadan-gadan da Hezbollah, Netanyahu ya ce idan buƙatar hakan ta taso, “za mu fuskanci wannan ƙalubalen shi ma. Za mu iya yin yaƙi daban-daban. Mun shiryawa hakan.”

Game da yaƙin Gaza, ya ce sun kusa kawo ƙarshen hare-hare masu tsanani, amma ba za su daina yaƙi ba sai sun ƙwace ikon yankin daga hannun Hamas.

Netanyahu ya ce Tel Aviv na son kafa wasu “ƙabilu 'yan ƙasa” domin gudanar da mulki a Gaza.

Kazalika ba zai "yiwu" Isra'ila ta sake kafa matsugunan 'yan-kama-wuri-zauna a Gaza.

Isra'ila ta shirya sauya tsari a Lebanon, in ji Netanyahu. / Hoto: AA

0200 GMT — Bama-bamai da Isra'ila ta harba a Birnin Gaza sun kashe ma'aikatan lafiya biyu

Falasɗinawa biyu da ke aiki da Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza sun mutu sannan da dama sun jikkata sakamakon wasu hare-haren bama-bamai ta sama da Isra'ila ta kai a wani ƙaramin asibiti a Birnin Gaza.

Rundunar 'yan bijilanti ta Gaza ta bayyana haka a wata sanarwa tana mai cewa “tawagarmu ta gano gawa guda biyu ta ma'aikatan lafiya da suka yi shahada sannan da dama sun jikkata yayin da jirgin sojojin mamaya ya kai hari a ƙaramin asibiti na Al Daraj,” ko da yake ba ta yi ƙarin bayani ba.

0021 GMT — Isra'ilawa sun jikkata a harin makamai masu linzami da aka kai musu daga kudancin Lebanon

Isra'ilawa biyu sun jikkata yayin da wasu makamai masu linzami da aka harba daga Lebanon suka faɗa wani gida.

“Mutum biyu sun samu rauni ba mai tsanani ba” sakamakon makamai masu linzami da aka harba waɗanda suka nufi birnin Metula na arewacin Isra'ila, a cewar gidan rediyon rundunar sojojin Isra'ila a saƙon da ya wallafa a shafin X.

Rahotanni sun ce wani helikwafta ya kwashe mutanen da suka jikkata inda ya kai su Cibiyar Lafiya ta Rambam da ke Haifa. Hukumomin Lebanon ba su ce komai kan batun ba.

TRT Afrika da abokan hulda