“Dakarun Isra'ila sun kashe mutane 41 tare da jikkata 103 a hare-haren ƙare-dangi da suka kai wa wasu iyalai a awanni 24 da suka wuce,” in ji sanarwar Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza / Hoto: AA

Asabar, 27 ga watan Yuli, 2024

1611 GMT — Sojojin Isra'ila sun kashe ƙarin Falasɗinawa 41 a hare-hare da suka kai a Gaza, abin da ya sa adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a yankin ya kai 39,258 tun daga 7 ga watan Oktoba, a cewar Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta yankin.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ƙara da cewa mutum aƙalla 90,589 ne suka jikkata sakamakon hare-haren.

“Dakarun Isra'ila sun kashe mutane 41 tare da jikkata 103 a hare-haren ƙare-dangi da suka kai wa wasu iyalai a awanni 24 da suka wuce,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa, “Har yanzu akwai mutane da dama a ƙarkashin ɓaraguzan gine-gine da kuma kan hanyoyi domin kuwa masu aikin ceto sun kasa isa gare su.”

1507 GMT — Akalla yara 15 da mata 8 na daga cikin Falasdinawa 31 da aka kashe a wani harin da Isra’ila ta kai a makarantar Khadija da ke Deir al-Balah da ke tsakiyar zirin Gaza, kamar yadda ofishin yada labaran gwamnatin Falasɗinawa ya sanar a ranar Asabar.

Tun da farko, ofishin yada labaran gwamnatin Gaza ya ce Falasdinawa 31 da suka hada da yara kanana ne suka mutu yayin da wasu 100 suka jikkata a lokacin da jiragen yakin Isra'ila suka kai hari a makarantar, wadda kuma ta kasance asibitin filin.

A cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran ya fitar ya bayyana cewa, makamai masu linzami guda uku sun afka wa wani wurin da ya kasance mafakar dubban mutanen da suka rasa matsugunansu.

Sojojin Isra'ila sun amince da kai harin a safiyar ranar Asabar, suna masu ikirarin cewa tana dauke da cibiyar kwamandojin kungiyar Hamas, a cewar wata sanarwa daga kakakin rundunar Avichay Adraee.

Sojojin Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a kullum waɗanda akasarinsu mata ne da yara. / Hoto: Reuters

0730 GMT — Sojojin Isra’ila sun bayar da umarni ga mazauna Khan Younis su yi hijira zuwa al-Mawasi da ke kudancin Gaza, wanda wuri ne da ake yin ikirarin cewa “mai aminci” ne, amma yana fuskantar hare-hare akai-akai.

A wata sanarwa da sojojin suka fitar, sun bayyana cewa “ci gaba da zama a wannan wurin hatsari ne” sakamakon “hare-haren rokoki” daga kudancin Khan Younis.

A ranar 13 ga watan Yuli ne sojojin Isra'ila suka kai hari kan sansanonin 'yan gudun hijirar a Al Mawasi, inda suka kashe Falasdinawa sama da 90 tare da jikkata wasu kusan 300 a cewar majiyoyin Falasdinawa.

2101 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla goma a hare-hare da ta kai ta sama a faɗin Gaza, in ji rundunar da ke kare fararen-hula ta yankin.

A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce an kashe Falasɗinawa shida tare da jikkata gommai a hari ta sama da Isra'ila ta kai a gidaje biyu, a garin Zawayda da ke tsakiyar Gaza da kuma kuma birnin Khan Younis da ke kudanci.

Kazalika a wata sanarwa ta daban, rundunar da ke kare fararen-hula ta Falasɗinu ta ce Isra'ila ta kashe Falasɗinawa biyu a wani hari ta sama da ta kai kan wani taron mutane a yankin Al-Kateeba da ke Khan Younis.

Haka kuma a sanarwa ta uku, rundunar ta ce dakarun Isra'ila sun kai samame a kan wani taron jama'a a yammacin Birnin Gaza inda suka kashe mutum biyu tare da jikkata wasu.

Sannan mutane da dama sun jikkata sakamakon luguden wuta da sojojin Isra'ila suka yi a wani gida a yammacin sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, a cewar rundunar da ke kare fararen-hula ta yankin.

2323 GMT — Amurka ta yi iƙirarin lalata jirage 6 marasa matuƙa na Houthi, jiragen ruwa 3 a Yemen

Rundunar sojin Amurka ta yi iƙirarin lalata jirage shida marasa matuƙa na Houthi a yankin da ƙungiyar ta mamaye da kuma jiragen ruwa uku da ke aiki a gaɓar tekun Yemen, kamar yadda Rundunar Bayar da Amurka ta Amurka (CENTCOM) ta bayyana.

"An yi amannar cewa waɗannan makamai suna barazana ga Amurka da dakarun da kuma jiragen ruwa na 'yan kasuwa," a cewar saƙon da CENTCOM ta wallafa a shafin X.

"An ɗauki matakin ne domin kare 'yancin walwala a cikin teku tare da tabbatar da tsaron teku ga masu jigila a cikinsa daga ƙasashen duniya," in ji sakon.

TRT Afrika da abokan hulda