Alhamis, 20 ga Fabrairun 2025
1320 GMT — Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya gayyaci shugabannin kasashen Larabawa na Gulf da kuma na Masar da Jordan don wani taro a Riyadh a ranar Juma’a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA ya ruwaito.
Kasashen Larabawa sun yi alkawarin yin aiki a kan wani shiri na bayan yaƙi na sake gina Gaza domin tunkarar shawarar shugaban Amurka Donald Trump na sake gina yankin da mayar da shi wurin shaƙatawa na gabar tekun kasa da kasa bayan sake tsugunar da mazaunanta Falasdinawa a wasu wurare.
Saudi Arebiya ta ce taron na ranar Juma'a zai kasance ba na hukuma ba kuma za a yi shi ne cikin "tsarin dangantakar 'yan'uwantaka da ke hada shugabannin," in ji SPA.
SPA ta kara da cewa, dangane da matakin da kasashen Larabawa suka dauka na hadin gwiwa da kuma shawarwarin da aka fitar dangane da shi, zai kasance cikin ajandar taron gaggawa na kasashen Larabawa da za a yi a 'yar'uwarmu Jamhuriyar Larabawa ta Masar," in ji SPA, yayin da yake magana kan shirin taron gaggawa na kasashen Larabawa da za a yi a ranar 4 ga watan Maris mai zuwa domin tattauna rikicin Isra'ila da Falasdinu.
Trump ya yi kira ga Masar da Jordan su karbi Falasdinawa da ba su wajen zama bayan fitar da su daga Gaza, shawarar da dukkansu suka yi watsi da ita.
0708 GMT — Hamas ta miƙa gawawwakin 'yan Isra'ila huɗu ga ƙungiyar Red Cross
Kungiyar Hamas ta mika gawawwakin mutum hudu ‘yan Isra’ila ga kungiyar agaji ta Red Cross waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su amma Isra’ilar ta kashe su a yayin da take kai hare-hare a Gaza.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta nufi wani wuri a Gaza domin karbar gawawwakin ‘yan Isra’ilan huɗu da aka shirya mikawa karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta, kamar yadda kafafen yada labaran Isra'ila suka rawaito.
Dakarun na Hamas sun miƙa gawawwakin Khan Younis da ke kudancin birnin Gaza. Gabanin miƙa su, ɗaruruwan mutane sun taru a wani wuri wanda a baya ake amfani da shi a matsayin maƙabarta.
An katange wurin domin nesantar da masu kallo daga ainahin wurin da aka miƙa gawawwakin ga ƙungiyar Red Cross.
2135 GMT — Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya sake jaddada cewa kasarsa ba ta sayarwa ba ce, kuma ya yi watsi da duk wani kira na a kori al'ummar Falasdinu.
Hakan ya zo ne a lokacin bude taron kwamitin kolin Fatah a Ramallah da ke tsakiyar Gabar Yammacin Kogin Jordan, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasdinu, WAFA.
Yayin da yake misali da halartar taron kungiyar Tarayyar Afirka a Addis Ababa da ya yi, wanda aka kammala ranar Asabar, Abbas ya bayyana cewa, ya jaddada matsayar Falasdinu kan duk wani yunƙuri na raba al'ummar Falasdinawa.
"Falasdinu ba ta sayarwa ba ce," in ji shi, yana mai nanata "tabbatacciyar matsayar Falasdinawa cewa ba wani yanki nata - ciki har da Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan, ko Kudus - da za a yi ƙwace."
Ƙarin labarai 👇
2345 GMT — Isra'ila ta ci gaba da yin watsi da alkawurran da ta dauka na tsagaita wuta: Sojojin Lebanon
Sojojin kasar Labanon sun zargi Isra'ila da ci gaba da kauce wa alkawurran da ta dauka karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma keta hurumin kasar Lebanon.
A martaninta na farko a hukumance game da mamayar da Isra'ila ke ci gaba da yi a yankunan kan iyaka guda biyar a kudancin Lebanon, sojojin sun tabbatar da cewa dakarunta na ci gaba da aikewa da su zuwa dukkan garuruwan da ke kan iyaka da ke kudancin kasar tare da hadin gwiwar kwamitin Quintet da ke sa ido kan yarjejeniyar tsagaita wuta da dakarun MDD a Lebanon (UNIFIL) bayan janyewar sojojin Isra'ila daga wadannan yankuna.
Rundunar sojin Isra'ila ta ci gaba da zama a wurare da dama na kan iyaka da ke cikin kasar Lebanon, suna ci gaba da kauce wa alkawuran da suka dauka tare da keta hurumin kasar Labanon ta hanyar ci gaba da cin zarafi ga tsaron kasar Lebanon da 'yan kasar.