‘Yan sandan na Indiya sun bayyana cewa sun aiwatar da wannan samamen ne sakamakon “bayanan sirri” da suka samu kan “sayarwa da rarraba wani rubutu mai tallata ƙungiyar da aka haramta. / Hoto: AP

‘Yan sandan Indiya a yankin Kashimir da ke ƙarƙashin Indiya, sun kai samame gomman shagunan sayar da littattafai inda suka ƙwace ɗaruruwan kwafi na littattafai da wani Malamin Addinin Musulunci ya rubuta, lamarin da ya jawo Malaman Musulunci a faɗin duniya suka harzuƙa.

‘Yan sandan na Indiya sun bayyana cewa sun aiwatar da wannan samamen ne sakamakon “bayanan sirri” da suka samu kan “sayarwa da rarraba wani rubutu mai tallata ƙungiyar da aka haramta.

Duk da cewa ‘yan sandan ba su bayyana sunan marubucin littafin ba, amma masu shagunan sun ce littattafan da aka ƙwace na Marigayi Abul Ala Maududi ne, wanda shi ne ya ƙirƙiro Jamaat-e-Islami, wadda ƙungiya ce ta Musulunci kuma jam’iyyar siyasa.

An raba yankin Kashmir tsakanin Indiya da Pakistan tun bayan samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya a shekara ta 1947, kuma dukkansu suna da'awar yankin Himalayan gaba daya nasu ne.

Kungiyoyin 'yan aware masu neman 'yancin yankin Kashmir ko hedkwatarta da Pakistan, sun shafe shekaru da dama suna fafatawa da sojojin Indiya, inda aka kashe dubbai a yayin rikicin.

Gwamnatin Firaiminista Narendra Modi ta ayyana reshen Jamaat-e-Islami na Kashmir a cikin 2019 a matsayin “haramtaciyyar ƙungiya”.

Modi da jam’iyyarsa sun yi fice a Indiya wurin yin kalamai na ƙin jinin Musulunci.

TRT World