Jiragen saman Isra'ila sun kai hari Damascus a karo na biyu cikin kwana biyu. / Hoto: Reuters / Photo: AP

Juma'a, 15 ga Nuwamban 2024

1256 GMT — Kafafen yada labaran gwamnatin Syria sun ce Isra’ila ta kai hari a gundumar Mazzeh da ke Damascus, wanda shi ne hari na biyu cikin kwanaki da dama da aka kai a unguwar da ofisoshin jakadanci, hedkwatar tsaro da kuma ofisoshin Majalisar Dinkin Duniya ke da su.

Kamfanin dillancin labaran SANA ya bayyana cewa, Isra'ila ta hare-haren a yankin Mazzeh da ke Damascus," bayan rahoton da ya bayar da na wani mummunan harin da Isra'ila ta kai a gundumar kwana daya da ya gabata.

0320 GMT –– Isra'ila ta kai hari ginin hukumar kare farar hula a Lebanon, ta kashe mutum 12

Akalla mutum 12 ne suka mutu a ranar Alhamis a wani harin da Isra’ila ta kai ta sama inda ta lalata ginin hukumar tsaron farar hula a garin Douris da ke gundumar Baalbek a gabashin Lebanon.

Harin ta sama "ya faɗa garin Douris, wanda ya haifar da rugujewar ginin Hukumar Tsaro ta Farar Hula da kuma lalata ginin da ke kusa," in ji Kamfanin Dillancin Labarai na Labanon.

Adadin waɗanda aka bayar da rahoton sun rasu tun farko mutum bakwai ne. An gano gawawwakin waɗanda suka rasu sannan an aika da su wurin ajiyar gawawwaki a asibitin gwamnati na Baalbek. Kamar yadda kamfanin dillancin labaran ya ƙara da cewa.

0124 GMT — Jami'in Hamas ya ce ƙungiyar ta shirya tsagaita wuta ba tare da ɓata lokaci ba

Wani jigo a kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ya jaddada cewa a shirye suke don cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sakin Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su a matsayin wani bangare na musayar fursunoni "mai tsanani".

Basem Naim, wani likitan Falasdinu, ɗan siyasa kuma jigo a ofishin siyasa na Hamas, ya ce "yarjejeniya mai kyau da aka fayyace ta ƙarshe" ita ce ranar 2 ga Yuli.

"An tattauna dalla-dalla, kuma ina tsammanin muna kusa da tsagaita wuta… wanda zai iya kawo karshen wannan yakin, ya kawo tsagaita wuta na dindindin da janyewa baki daya da kuma musayar fursunoni," in ji shi a wata hira da Sky News.

Naim ya ce "Abin takaici, (Firaministan Isra'ila Benjamin) Netanyahu ya gwammace ya bi ta wata hanya" ya kuma tunatar da cewa "Isra'ila ta yi kisan kiyashi akalla biyu zuwa uku" a Khan Younis da kuma birnin Gaza bayan haka.

Dangane da kisan gillar da aka yi wa shugaban ofishin siyasa na Hamas Ismail Haniyeh a watan Yuli, ya ce tun bayan hakan, ba su sami "wata sahihiyar magana ba."

Karin bayani 👇

0003 GMT — Bam da aka harba daga Lebanon ya raunata sojojin Isra'ila 2

Sojojin Isra'ila biyu sun jikkata sakamakon fashewar wani jirgin mara matuki da aka harba daga kudancin Lebanon zuwa arewacin Isra'ila, a cewar rundunar.

Jaridar Yedioth Ahronoth ta bayar da rahoton cewa, jirgin mara matuki ya fado kuma ya fashe a sansanin Eliakim da ke kudancin Haifa bayan da sojojin tsaron saman Isra'ila suka fatattake su na kusan mintuna 40.

TRT World