1558 GMT — Isra'ila za ta fara 'dakatawa' da kai hari na tsawon awa hudu kowace rana a Gaza — Amurka
Isra'ila ta amince ta dinga dakata kai hare-hare cikin Gaza na tsawon awa huɗu a kowace rana don bai wa mutane damar tserewa daga yaƙin, a cewar Fadar White House.
"Isra'ila za ta fara aiwatar da dakatar da buɗe wuta ta tsawon sa'o'i hudu a yankunan arewacin Gaza a kowace rana, tare da bayar da sanarwar sa'o'i uku kafin hakan," kamar yadda mai magana da yawun kwamitin tsaron kasar John Kirby ya shaida wa manema labarai.
"Mun yi amanna cewar wannan dakatawar wani mataki ne na hawa madaidaiciyar hanya, musamman ma don tabbatar da cewa fararen hula za su samu damar tserewa zuwa yankuna masu aminci da ke nesa daga inda ake yaƙin," ya ce.
Dakatawar ɗan lokacin za kuma ta ba da damar shigar da kayan jinƙai cikin yankunan da ake so tare da bai wa Falasɗinawa ficewa salin alin," a cewar Kirbi.
1334 GMT — Isra'ila na ci gaba da kai hare-haren sama a yankunan kudancin Lebanon
Isra'ila ta ci gaba da luguden wuta a bayan garuruwan kan iyaka da ke kudancin Lebanon da makaman atilare da jirage marasa matuƙa, ba tare da an samu asarar rai ba, a cewar wakilin Anadolu.
An yi ruwan bama-bamai a wajen Rmeish da Ramia, yayin da wani jirgi mara matuƙi ya dinga kai nasa harin a garin Mahibib.
Sannan an yi ta kai harin yankunan da ke wajen kan iyakar garin Habbariya. Jirage marasa matuƙan sun ci gaba da shawagi a sassan tsakiya da gabas.
1304 GMT — Shugabannin Mossad da CIA sun gana da Firaministan Qatar kan yarjejeniyar sakin wadanda ake garkuwa da su a Gaza
An gudanar da wani taro na ɓangarori uku a Doha tsakanin shugabannin hukumar leƙen asiri ta Amurka CIA da ta Isra'ila Mossad da kuma firaministan Qatar.
Sun yi ganawar ne don tattauna ma'aunan da ya kamata a duba don cimma yarjejeniyar sakin mutanen da ake garkuwa da su da kuma dakatar da hare-haren da ake kai wa Gaza, kamar yadda wata majiya da aka yi wa bayanin yadda taron ya gudana ta shaida wa Reuters.
Muhimmancin taron shi ne don dukkan ɓangarorin uku su zauna a lokaci guda don a gaggauta aiwatar da yarjejeniyar, in ji majiyar.
Batutuwan da aka tattauna sun haɗa da bayar da damar shigar da kayayyakin agaji da fetur cikin Gaza.
1230 GMT — Macron ya nemi a 'tsagaita wuta' a taron neman tallafi kan Gaza
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bukaci kasashe da "su yi kokarin ganin an tsagaita wuta" tsakanin Isra'ila da Hamas a Gaza.
Ya bayyana haka ne a yayin da yake bude fara babban taron neman taimaka wa Falasdinawa da ake gudanarwa a Paris.
Macron ya sanar da mahalarta taron cewa "A yanzu, muna bukatar kare rayukan fararen-hula. Domin yin hakan, muna bukatar a dan tsagaita don gudanar da ayyukan jinkai, kuma dole mu yi aiki don tabbatar da tsagaita wuta."
1026 GMT — Sojojin Isra'ila da mayakan Hamas suna fafatawa a kan titunan Gaza
Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare ta sama a Gaza a yayin da sojojin kasar suke bi layi-layi suna fafatawa da mambobin kungiyar Hamasa, sannan dubban Falasdinawa da ke neman mafaka suna ta tserewa zuwa kudancin Gaza.
Dubban Falasdinawa sun makale a yankin cikin "mawuyacin hali" a yayin da Isra'ila ta kwashe sama da wata daya tana kai musu hare-hare ta sama da kasa ba tare da samun isasshen abici da ruwa ba, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha yin fatali da tayin tsagaita wuta yana mai cewa ba zai daina ba sai Hamas ta saki mutanen da ta yi garkuwa da su a Gaza.
A cewar wasu jami'ai, ana tattaunawa domin sakin mutum 12 da aka yi garkuwa da su, ciki har da Amurkawa shida, kafin a yarda a tsagaita wuta ta kwana uku.
0749 GMT — Manyan motoci 187 dauke da kayan agaji sun isa Gaza
Kugiyar agaji ta Palestine Red Crescent Society ta ce tawagar manyan motoci 187 dauke da kayan agaji ta isa yankin Gaza da aka yi wa kawanya daga Mashigar Rafah.
A wata sanarwa, ta ce tawagarta ta karbi manyan motoci 187 dauke da kayan agaji daga kungiyar agaji ta Egyptian Red Crescent, tana mai cewa ta karbi motoci 81 ranar Laraba yayin da ta karbi motoci 106 a yau Alhamis, da kuma motoci biyar na daukar marasa lafiya daga Kuwait.
Ta kara da cewa duk da hana shigar da fetur yankin, motocin na dauke da magunguna da abinci da ruwa da sauran kayan agaji.
0600 GMT — Isra'ila ta sake kai harin bama-bamai a Asibitocin Al Shifa da Al Nasr na Gaza
Jiragen yakin Isra'ila sun yi luguden wuta a Asibitin Al Shifa da Asibitin Yara na Al Nasr da ke Gaza.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Falasdinawa WAFA, Isra'ila ta harba rokoki a Asibitin Al Shifa, inda dubban majinyata da 'yan gudun hijira suke samun mafaka.
Harin da jiragen suka kai kusa da Asibitin Yara na Al Nasr da ke yammacin Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa uku da jikkata da dama.
0509 GMT — Amnesty International ta nemi Isra'ila ta kawo karshen 'rashin imani' a kan Falasdinawa a Gabar Yammacin Kogin Jordan
Hukumomin Isra'ila suna kara yin amfani da tsarin daure Falasdinawa ba bisa ka'ida ba a Gabar Yammacin Kogin Jordan kuma sun ki yin bincke kan zargin gallazawa da kashe wadanda suka daure, a cewar kungiyar kare hakkin Dan'adam ta Amnesty International a ranar Laraba.
A yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare Gaza, Amnesty International ta ce ana gallaza wa fursunoni Falasdinawa da take hakkokinsu da daure su ba bisa ka'ida ba.
"Kazalika sun bullo da wani tsari na daure mutane cikin ‘gaggawa’ da ya ba su ikon musguna wa Falasdinawa da nuna musu rashin imani," in ji kungiyar a sakon da ta wallafa a shafin X.
Ta jaddada kiran da ta yi na sakin fursunoni nan-take.
0430 GMT — Sanatan Amurka ya ce fararen-hula da ake kashewa a Gaza 'sun yi yawa'
Wani dan Majalisar Dattawan Amurka ya ce yana da "muhimmanci" Isra'ila ta rika yin taka-tsantsan wurin kai hare-hare Gaza domin ta rage kisan fararen-hula.
"Ina gani fararen-hula da ake kashewa sun yi matukar yawa kuma akwai bukatar a yi taka-tsantsan," a cewar Chris Murphy, Sanata na jam'iyyar Democrat kuma mamba a Kwamitin Harkokin Kasashen Waje na Majalisar, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.
"Ina matukar damuwa kan tsarin Isra'ila kuma idan har burinta shi ne ta kawar da Hamas, to kisan da take yi wa fararen-hula, wanda ke zubar da kimarta, ya kamata a rage shi."
Hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa ta sama da kasa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 10,600, galibinsu fararen-hula, a cewar Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza.