Isra'ila ta harba bama-bamai a Rafah na Gaza duk da tsagaita wuta da aka cim ma / Hoto: Reuters / Photo: AA

Litinin, 20 ga Janairu, 2025

1539 GMT — Mamayar gaba daya ko wani bangare na yankin Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ke yi “zai zama babban cin zarafi da take dokokin kasa da kasa,” kamar yadda Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadin.

Guterres ya yi tir da kalaman jami’an Isra’ila da ke nuna irin wannan matakin.

"Na damu matuka game da wata barazana da za a iya fuskanta ga mutunci da martabar yankin Falasdinawa da aka mamaye na Gaza da Gabar Yammacin Kogin Jordan," kamar yadda ya shaida wa taron kwamitin sulhu na MDD kan yankin Gabas ta Tsakiya.

Ya yi nuni da "sauye-sauyen harkokin gudanarwa na Isra'ila" a cikin biyun da suka gabata cikin shekaru biyu da suka gabata.

1210 GMT — Isra'ila ta harba bama-bamai a Rafah na Gaza duk da tsagaita wuta da aka cim ma

Wasu Falasdinawa uku sun jikkata sakamakon wani gurneti da wani jirgin yakin Isra'ila mara matuki ya jefa a gabashin Rafah da ke kudancin Gaza, kamar yadda wata majiyar lafiya ta sanar.

Majiyar ta ce, an kai harin ne a lokacin da Falasdinawan uku ke duba gidajensu da ke kusa da yankin da ke gabashin birnin Rafah.

A cewar shaidu, sojojin Isra'ila an jibge a yankunan gabashin Rafah da ke kan iyaka, inda suke hana Falasdinawa tunkarar yankin karkashin matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni a Gaza.

0828 GMT — Manyan motoci fiye da 630 sun shigar da kayan agaji cikin Gaza — MDD

Jami'an jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya sun ce manyan motoci fiye da 630 ɗauke da kayayyakin agaji sun shiga Gaza da aka yi wa ƙawanya, a wani mataki na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma tsakanin isra'ila da Hamas.

A wani saƙo da aka wallafa a shafin X, ƙaramin sakatare na ayyukan jinƙai na MDD, Tom Fletcher ya ce fiye da manyan motocin kaya 630 ne suka shiga Gaza a ranar Lahadi, inda aƙalla 300 daga cikinsu suka shigar da kayan agaji cikin arewa.

Fletcher ya rubuta cewa, "Ba za mu ɓata lokaci ba."

2335 GMT — Isra'ila ta saki Falasɗinawa fursunoni 90

Hukumar kula da gidajen yarin Isra'ila ta ce ta kammala sakin Falasɗinawa fursunoni 90, a wani ɓangare na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza wadda ta soma aiki ranar Lahadi.

"An saki dukkan fursunoni daga gidan yarin Ofer da kurkukun Birnin Ƙudus", in ji wata sanara da hukumar ta fitar kafin ƙarfe 1:30 na dare.

Wata babbar motar ɗaukar kaya, ɗauke da gomman fursunonin, dukkansu mata da ƙananan yara, ta fita daga kurkukun Ofer da ke wajen birnin Ramallah na Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.

Dukkan waɗanda aka saka mata da ƙananan yara ne, a cewar wani jadawali a Hukumar Kula da Harkokin Gudanarwar Falasɗinawa.

0244 GMT — Gazawar Isra'ila ta cim ma burinta ne ta tilasta mata amincewa a tsagaita wuta: Hamas

Gazawar Isra'ila ta cim ma burinta ne ta tilasta mata sassauta ra'ayinta a teburin sulhu, a cewar Mohammad Nazzal, wani babban jami'i a fannin siyasa na ƙungiyar Hamas.

"Burin Isra'ila shi ne ta kuɓutar da mutanenta da aka yi garkuwa da su, ta rusa masu gwagwarmaya — musamman Hamas — sannan ta mamaye ɗaukacin Gaza. Babu ɗaya daga cikin muradunta da ya biya," in ji Nazzal a keɓantacciyar tattaunawa da Anadolu Agency.

"Sun kasa yin amfani da ƙarfin soji don kuɓutar da mutanensu da aka yi garkuwa da su don haka sai suka sassauta matsayinsu a lokacin tattaunawa. A halin da ake ciki, babu yadda za a kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su idan ba ta hanyar sulhu ba," a cewarsa.

2352 GMT — Falasɗinawa a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan sun yi murnar dawowar 'yan'uwansu

Dandazon mutane sun taru a garin Beitunia da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan inda suka riƙa murnar sakin 'yan'uwansu daga gidajen yarin Isra'ila.

TRT World