"Da alama hare-haren da Isra'ila take kaiwa ba su da ranar tsagaitawa," in ji ƙwararru na MƊD. / Hoto: AA

Talata, 28 ga Janairu, 2025

0204 GMT — Wata ƙungiya ta ƙwararru na MDD ta bayyana damuwa game da hare-haren da Isra'ila take kai wa a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, tana mai gargaɗi cewa matakin yana cike da "hatsari na ƙara ruruta wutar" yaƙin da take yi da Falasɗinawa.

A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta yi kira ga ƙasashen duniya su ɗauki mataki na kare hakki da mutuncin al'ummar Falasɗinu.

"Mun yi matuƙar kaɗuwa da ganin yadda hare-hare suke watsuwa Jenin da sauran yankunan da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan," in ji su.

2023 GMT — Isra'ila ta kashe wata yarinya Bafalasɗiniya, ta jikkata mutum 3 da ke kan hanyar komawa Arewacin Gaza

Isra'ila ta kashe wata yarinya Bafalasɗiniya tare da jikkaTA mutum uku a hari ta sama da dakarunta suka kai kan Falasɗinawa 'yan gudun hijira da ke kan hanyar al Rashid domin komawa Gaza.

Asibitin Al Awda da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat a tsakiyar Gaza ta fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da kisan, yana mai cewa: "Wata yarinya Bafalasɗiniya ta yi shahada, yayin da mutum uku suka jikkata sakamakon hari ta sama da Isra'ila ta kai wa Falasɗinawa 'yan gudun hijira da ke bin hanyar al Rashid domin komawa arewacin Gaza."

Mahaifiyar yarinya 'yar shekara 5 da dakarun Isra'ila suka kashe tana alhinin rasuwar 'yarta a asibitin Awda da ke Birnin Gaza / Photo: AA

Ƙarin labarai👇

2316 GMT — Rubio ya tattauna da Sarki Abdullah na Jordan kan yarjejejiyar tsagaita wuta a Gaza

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya yi wayar tarho da Abdullah na Jordan, kwanaki kaɗan bayan shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da shawarar kwashe Falasɗinawan da ke Gaza zuwa ƙasashen Jordan da Masar .

"Sakataren Harkokin Wajen Amurka da Sarki Abdullah sun tattauna kan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su, da samar da wata hanya ta tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin," in ji wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar.

Sai dai sanarwar ba ta ambaci shawarar da Trump ya bayar ba.

TRT World