1205 GMT— Isra'ila ta kashe ƙarin ƴan jarida biyu a Gaza
Isra’ila ta kashe ƴan jarida biyu a Zirin Gaza, wanda hakan ya kawo jumullar adadin ƴan jaridar da ƙasar ta kashe tun daga 7 ga watan Oktoba zuwa 140, kamar yadda Ma’aikatar Watsa Labarai ta Gaza ta tabbatar a ranar Laraba.
Mohammad Al-Sayyed Abu Skheil da Tareq Abu Skheil, waɗanda masu ɗaukar rahoto ne na gidan rediyon Al-Quds Voice Radio, sun rasu ne a lokacin da Isra’ila ta kai hari a asibitin Al-Shifa da ke Gaza, kamar yadda ofishin watsa labaran ya tabbatar a wata sanarwa a ranar Laraba.
Sojojin na Isra’ila sun janye daga asibitin a ranar Litinin da safe bayan sun shafe mako biyu a wurin. Sojojin sun kashe gomman mutane a asibitin baya ga lalata wurare a cikin asibitin.
1104 GMT — Adadin mutanen da Isra’ila ta kashe a Gaza ya kusa 33,000
Adadin mutanen da Isra’ila ta kashe a Falasɗinu ya ƙaru zuwa 32,975 tun daga Oktobar bara, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu ta tabbatar.
Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta fitar da sanarwar a lokacin da aka shiga rana ta 180.
Hare-haren da ake kaiwa a Gazar ya yi sanadin mutum 75,577 sun samu rauni, kamar yadda ta ƙara da cewa.
Ma’aikatar ta ce a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, Isra’ilar ta kashe mutum 59 da raunata 83 a faɗin Gaza.
2130 GMT — Falasɗinawa sun sake bijiro da buƙatar neman kujerar dindindin a MDD ana tsaka da yaƙin Isra'ila
A hukumance yankin Falasɗinu ya sake bijiro da buƙatar neman zama mamba na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, a cewar wata wasiƙa daga wakilinsu a MDD.
"Bayan na samu umarni daga shugabannin Falasɗinawa, ina sake miƙa buƙata ga Kwamitin Tsaro a watan Afrilu na 2024 don a ba mu matsayin mamba ta dindindin," in ji wasiƙar da Riyad Mansour ya aika wa Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, wadda aka miƙa wa Kwamitin Tsaro.
Falasɗinawa, waɗanda suke matsayi na ƴan-kallo tun shekarar 2012, sun kwashe shekaru da dama suna neman a ba su matsayin mamba na dindindin, lamarin da ke nufin a amince da yankin a matsayin ƙasa mai yancin kanta, kasancewa galibin ƙasashe mambobin majalisar sun yarda ta ita a matsayin ƙasa.
Masu sharhi na ganin zai yi wahala buƙatar ta Falasɗinu ta samu karɓuwa domin kuwa Amurka, babbar ƙawar Isra'ila, tana iya yin amfani da ƙarfinta a Kwamitin Tsaro don hawa kujerar na-ƙi.
Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa da Ƙungiyar Ƙasashe Musulmai da kuma Ƙungiyar Ƙasashe ƴan ba-ruwanmu sun aike da wasiƙa ga Sakatare Janar ma MDD ranar Talata, inda suka goyi bayan kasancewar Falasɗinu a matsayin mamba ta majalisar.
"Muna so mu jawo hankalinka cewa, a wannan ranar, mambobi 140 sun amince d kasancewar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ƴancin kanta," a cewar wasiƙar haɗin-gwiwa da ƙasashen suka aika wa shugaban majalisar.
0106 GMT — Isra'ila ta ce kisan da ta yi wa ma'aikatan agaji 'babban kuskure be'
Shugaban sojojin Isra'ila ya ce kisan da dakarunsu suka yi wa ma'aikatan agaji bakwai a Gaza "babban kuskure ne", bayan sun sha suka daga ƙasashen duniya.
"Wannan lamari babban kuskure ne," in ji shugaban sojojin Isra'ila Herzi Halevi a wanisaƙon bidiyo da ya fitar kan kisan da sojojinsu suka yi wa ma'aikatan World Central Kitchen (WCK) ranar Litinin.
"Bai kamata a ce hakan ya faru ba," a cewar Halevi, a yayin da ya ɗora alhakin kisan kan "kuskure -— wanda ya faru saboda an kai harin ne da daddare".
"Muna neman gafara ga mambobin WCK game da illar da muka yi ba tare da niyya ba."