Jirgin yakin Isra’ila ya shafe dare yana luguden wuta a Gaza da Isra’ila ta mamaye, inda dakarun Falasdinu su kuma ke ci gaba da harba makaman roka daga cikin birnin a daidai lokacin da rikicin ya shiga kwana na biyar.
Ana ci gaba da wannan rikicin duk da kokarin da kasar Masar ke yi na sulhu tsakanin bangarorin biyu.
Zuwa yanzu rikicin ya yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 33 da kuma dan Isra’ila daya tun bayan da rikicin ya barke ranar Talata a lokacin da dakarun Isra’ila suka kaddamar da yaki kan Falasdinawan.
Dakarun na Isra’ila sun yi hakan ne sakamakon zargin da suke yi cewa Falasdinawan na da niyyar kai hare-hare.
Sojojin Isra’ila sun ce sun kai hari kan cibiyoyin mayakan da ke ikirarin jihadi da kuma wuraren harba rokokinsu a harin da suka kai na tsakar dare wayewar garin Asabar.
Wani bidiyo mai duhu amma da haske mai ruwan toka ya nuna yadda ababe ke fashewa da kuma yadda hayaki ya turnuke samaniya daga wuraren da aka kai harin.
Bayan wasu sa’o’i, mayakan Gaza sun harba makaman roka, lamarin da ya ja jiniya ta soma kara da kuma tilasta wa wasu jama’ar Isra’ila hijira zuwa wasu garuruwa da ke kan iyaka domin guje wa bam.
Akalla mata hudu da kuma yara shida aka tabbatar da mutuwarsu a Gaza da ke da jama’a da kuma Isra’ila da Masar suka mamaye tun a 2007.
Isra’ila ta bayyana cewa Falasdinawa hudu ne suka rasu sakamakon kuskuren da Falasdinawan suka yi wurin harba makaman rokansu, lamarin da Falasdinawan suka musanta.
An kashe manyan kwamandojin da ke ikirarin jihadi tun bayan da aka soma wannan rikicin a ranar Talata.
Kungiyar ta harba sama da rokoki 1,000, wasu har can cikin Isra’ila. Wata mace daya ta mutu a lokacin da makamin na roka ya fada cikin wani gida da ke gefen Tel Aviv.
Rikici mafi muni tun Agusta
Rikicin tsakanin Isra’ila da Falasdinu ya tsawaita sama da shekara guda tun bayan barkewarsa inda lamarin ya yi sanadin mutuwar sama da Falasdinawa 140 da kuma ‘yan Isra’ila 19 da kuma wasu ‘yan kasashen waje tun watan Janairu.
A wannan makon ne Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya amince da matakin cigaba da kai hari ta sama kan Gaza.
Mista Netanyahu dai ya koma kan mulki ne a watan Disamba tare da abokansa masu tsatsauran ra’ayin akidar Orthodox ta Yahudanci.
Rayuwar yau da kullum ta tsaya cik a birnin da ke gefen teku wanda mayakan Hamas ke iko da shi, a dayan bangaren kuma Isra’ila ta shaida wa ‘yan kasarta da ke kusa da Gaza su zauna kusa da mafakar da aka tanada domin kare harin bam.
Rikicin wannan makon shi ne mafi muni tun bayan barkewar rikicin a watan Agusta inda aka kashe Falasdinawa 49 cikin kwana uku na yakin da ake yi da masu ikirarin jihadi da Isra’ila.