"Za a yi amfani da duk dabarun da suka dace wajen kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su," a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida na Pakistan. / Hoto: Reuters

Jami'an tsaro a yankin kudu maso yammacin Pakistan sun bazama neman 'yan wasan kwallon kafa shida da aka sace a makon jiya, a cewar ministan harkokin cikin gida na kasar.

An sace 'yan wasan ne a garin Sui da ke gundumar Dera Bugti na lardin Balochistan a kan hanyarsu ta zuwa gasar kwallon kafa ta cikin gida.

"An killace yankin gaba dayansa", a cewar sanarwar da Ministan harkokin cikin gida Sarfaz Bugti ya fitar a yammacin ranar Lahadi.

"Za a yi amfani da duk dabarun da suka dace wajen kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su," a cewar Ministan.

Lardin Balochistan mai arzikin albarkatun kasa, ya kasance yanki mafi girma da kuma karancin jama'a a Pakistan, ya kuma shafe shekaru da dama yana fama da tashe-tashen hankula.

TRT World