Dakarun Isra'ila sun kashe mutum 60 sun kuma jikkata wasu 280 in 'kisan kiyashi' biyar da aka yi wa iyalai a Gaza a cikin sa'o'i 24 da suka gabata. / Hoto: AA

1445 GMT Rundunar sojojin Isra'ila ta tabbatar da cewa dakarunta na aiki a tsakiyar birnin Rafah a faɗaɗa hare-haren da take yi a kudancin birnin Gaza.

Sanarwar ba ta yi ƙarin bayani kan wajen da ta ke aikin ba a tsakiyar Rafah, sai dai wata sanarwa gabanin wannan da kuma shaidu sun nuna cewa hare-haren na faruwa a sansanin 'yan gudun hijira na Shaboura da kuma wasu wurare a kusa da birnin.

Fiye da Falasɗinawa miliyan ɗaya ne suka guje wa birnin tun bayan fara kai hare-hare, kuma mutanen sun warwatsu a wuraren kudanci da tsakiyar Gaza.

1419 GMT Adadin mutanen da suka mutu a Gaza daga hare-haren Isra'ila ba ƙaƙƙautawa tun daga Oktoban bara ya kai 36,284, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Zirin Gaza da aka killace.

An kuma jikkata aƙalla wasu mutum 82,057 a hare-haren, kamar yadda ma'aikatar ta bayyana.

"Dakarun Isra'ila sun kashe mutum 60, sun kuma jikkata wasu 280 daban a wani 'kisan kiyashi' da aka yi wa iyali biyar a cikin sa'o'i 24 da suka gabata," a cewar ma'aikatar.

1045 GMT — Isra'ila ba za ta dain yaƙi a Gaza har sai Hamas ta saki mutanen da take garkuwa da su: Babban mai ba da shawara kan tsaro

Gwamnatin Isra'ila ba za ta kawo ƙarshen yaƙinta a Gaza ba idan har Hamas ba ta saki dukkan mutanen da take garkuwa da su ba tun ranar 7 ga watan Oktoban bara, a cewar Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro Tzachi Hanegbi.

Hanegbi ya faɗi hakan ne a yayin da yake ganawa da iyalan Isra'ilawan da ake garkuwa da su.

Ya ce nan ba da jimawa ba za a cimma "matakin farko" na yarjejeniyar dawo da mutanen da ake garkuwa da su ɗin, wacce aka sanya ta a ƙarƙashin dalilan jinƙai, kamar yadda tashar Channel 12 da kuma jaridar Times of Israel suka rawaito.

Sai dai rahotanni sun ce Hanegbi ya shaida wa iyalan cewa: "Wannan gwamnatin ba za ta daina yaƙin nan ba don a dawo da mutanen da ake garkuwa da su ɗin."

Sannan ya gaza faɗar wani shirin idan har ba a dawo da mutanen ba a lokacin da ake sa rai.

1050 GMT — Agaji 'ba ya isa wurin mutane' da ke Gaza, 'yara suna cikin masifar yunwa' — MDD

Ofishin bayar da agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya da Hukumar Lafiya ta (WHO) sun yi gargaɗi cewa agaji "ba ya isa wurin mutanen da ke" Gaza, kuma hakan ya sa yara sun faɗa cikin "bala'in yunwa."

"Tabbas ba ba sa samun agajin da suke matuƙar buƙata domin kauce wa kamuwa da tamowa," a cewar Jens Laerke, kakakin Ofishin bayar da agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya, a wurin wani taron MDD a Geneva.

Da yake bayani game da yiwuwar Isra'ila ta ƙwace Mashigin Philadelphi, Laerke ya ce: "Ƙarin kai hare-hare ba zai taimaka wa aikin bayar da agaji ba."

Ya ƙara da cewa abu ne mai "wahala a yi hasashen" yadda hakan zai shafi aikin bayar da agaji bak ɗaya, idan aka yi la'akari da "yadda yanayi yake sauyawa" a yankin inda dakarun tsaro suke motsawa daga wani waje zuwa wani.

"Muna so a daina kai hare-hare baki ɗaya. Hakan ne kawai zai ba mu damar gudanar da ayyukanmu yadda suka kamata."

2238 GMT —Wani harin haɗin-gwiwa na Amurka da Birtaniya ya kashe mutum biyu a Yemen

Sojojin Amurka da na Birtaniya sun sanar cewa sun kai hare-hare kan mayaƙan Houthi da ke Yemen. Ranar Alhamis kafar watsa labarai ta Houthi ta tabbatar da kisan aƙalla mutum biyu a hare-haren.

Ma'aikatar tsaron Birtaniya ta ce an kai hare-haren na haɗin-gwiwa ne a wurare uku a birnin Hodeidah da ke gaɓar Bahar Maliya.

Gidan talbijin na Al Masirah wanda ƙungiyar Houthi take gudanar da shi ya ruwaito cewa an kashe aƙalla mutum biyu sannan aka jikkata mutum 10 a hare-haren da aka kai a wani gini na gidan rediyo a lardin Al-Hawk na birnin Hodeidah.

Jirgin yaƙin Birtaniya samfurin RAF Typhoons yana cikin jiragen da suka kai hari kan mayaƙan Houthi a Yemen. / Hoto: X

0340 GMT — 'Yan majalisa na jam'iyyun adawa a Faransa sun yi kira a ƙaurace wa wani gidan talabijin saboda ya yi hira da Netanyahu

'Yan majalisar dokokin Faransa na jam'iyyun adawa sun yi kira a ƙaurace wa gidan talbijin na LCI bayan ya watsa wata hira da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ranar Alhamis.

An watsa hirar ce a wani shiri mai suna Le 20h de Darius Rochebin, a talbijin na LCI, mallakin gamayyar kamfanoni ta TF1 Group.

'Yan siyasa na jam'iyyun adawa da masu amfani da soshiyal midiya sun nuna matuƙar rashin jin daɗinsu kan watsa hirar, inda suka bayyana Netanyahu a matsayin "mai kisan kai," "mai kisan kiyashi" kuma "wanda ya aikata laifukan yaƙi."

TRT Afrika da abokan hulda