Ma'aikatar addini ta Gaza ta ce ana bukatar kusan dala miliyan 500 domin sake gina wadannan masallatai. / Hoto: Reuters

0225 GMT — Isra’ila ta lalata masallatai sama da 1,000 a Gaza da kashe masu wa’azi sama da 100

Isra’ila ta lalata masallatai 1,000 a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

“Sake gina wadannan masallatan zai ci kudi kimanin dala miliyan 500,” kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Addini da ke Gaza ta bayyana a wata sanarwa.

Akwai kimanin masallatai 1,200 a Zirin Gaza. Ma’aikatar ta ce Isra’ila ta kashe malamai masu wa’azi sama da 100 tun bayan soma wannan yakin.

1155 GMT — Sojan Isra'ila da ya yi yaki a Gaza ya kashe abokinsa a Tel Aviv

Wani sojan Isra’ila wanda bai jima da dawowa daga yaki a Gaza ba ya kashe abokinsa a Tel Aviv, kamar yadda kafafen watsa labarai na Isra’ila suka bayyana.

Kafar watsa labarai ta Channel 12 ta bayyana cewa sojan ya bi abokin nasa har gidansa inda ya kashe shi.

Kafafen watsa labaran Isra’ila a cikin ‘yan kwanakin nan sun ruwaito cewa akwai dubban sojoji wadanda suka je yaki Gaza suka dawo da ke fuskantar matsalar kwakwalwa.

Isra'ila na ci gaba da yin luguden wuta kan gidajen Falasdinawa musamman a Gaza. / Hoto: Reuters

1139 GMT — Isra'ila ta kashe karin mutum 178 a Gaza

Isra'ila ta kashe karin Falasinawa 178 da kuma raunata 293 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya da ke Gaza ta tabbatar.

Ko a jiya Asabar sai dai ma'aikatar ta ce sojojin na Isra'ila sun kashe 165 tsakanin Juma'a zuwa Asabar.

Zuwa yanzu Isra'ila ta kashe Falasdinawa 25,105 da kuma raunata 62, 681 tun daga 7 ga watan Oktoba.

AA
AFP
AP
Reuters