Talata, 3 ga watan Disamba, 2024
0755 GMT — Gaza na fuskantar rashin abinci 'irinsa mafi girma': MDD
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗi game da ƙarancin abinci a Gaza, inda ta bayyana lamarin a matsayin “irinsa mafi muni” sakamakon ƙawanyar da Isra'ila ta yi wa yankin.
“A yau, ana fuskantar ƙarancin abinci a faɗin Zirin Gaza a wani mataki mafi muni, kuma abincin da ake kai wa ya yi matuƙar raguwa,” in ji Beth Bechdol, Mataimakiyar Darakta-Janar ta Hukumar Abinci da Aikin Gona ta MDD a wani taro da aka gudanar a birnin Alƙahira na Masar.
Wasu daga cikin mazauna arewacin Gaza sun ce kayayyakin da suke amfani da su na yau da kullum sun ƙare baki ɗaya, lamarin da ke nuna irin mawuyacin halin da ake ciki.
Ƙarin labarai 👇
0921 GMT — Isra'ila ta kashe mutum 14 a arewacin Gaza, ta umarci mutane su fice daga kudanci
Dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla 14 a faɗin Gaza, yawancinsu a garin Beit Lahiya da ke arewacin yankin, a cewar ma'aikatan kiwon lafiya, a yayin da sojojin suka bayar da umarni ga mutane su fice daga kudancin yankin.
Ma'aikatan kiwon lafiya sun ce an kashe mutu takwas a hare-haren da Isra'ila ta kai a Beit Lahiya yayin da aka kashe mutum huɗu a wani yanki na Birnin Gaza.
Kazalika wani hari ta sama da Isra'ila ta kai ya kashe mutum biyu tare da jikkata wasu a Jabalia, babban sansanin 'yan gudun hijira na Gaza, in ji ma'aikatan asibiti.
0836 GMT — Hamas da Fatah sun amince su kafa kwamitin haɗin gwiwa domin gudanar da lamuran Gaza bayan yaƙi
Ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinu Hamas da ƙungiyar Fatah ta Shugaba Mahmud Abbas sun amince su kafa wani kwamiti na haɗin gwiwa domin tafiyar da harkokin Gaza idan an kammala yaƙi,in ji masu shiga tsakani daga ɓangarorin biyu.
A wannan tsari, wanda ke buƙatar amincewar Abbas, kwamitin zai ƙunshi mutum 10 zuwa 15 'yan-ba-ruwanmu waɗanda za a ɗora wa nauyin gudanar da harkokin tattalin arziki, lafiya da jinƙai da kuma sake gina yankin, kamar yadda daftarin da aka fitar kan lamarin wanda kamfanin dillanacin labarai na AFP ya gani.