Isra'ila ta kashe fiye da Falasdinawa 4,741 sannan ta jikkata 15,898 a hare-haren da take kai wa Gaza kawo yanzu, in ji Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu. Hoto: AFP

1830 GMT — Isra'ila ta kashe ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya 29 a Gaza

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da Falasdinawa 'yan gudun hijira ta ce Isra'ila ta kashe ma'aikatanta 29 tun lokacin da ta soma luguden wuta a Gaza.

"Muna cikin kaduwa da alhini. Yanzu an tabbatar da mutuwar abokan aikinmu 29 a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba," in ji hukumar a sakon da ta wallafa a shafinta na X, wanda a baya ake kira Twitter, bayan ta fitar da alkaluman ma'aikatanta 17 da suka mutu ranar Asabar.

Ta kara da cewa rabin mutanen da aka kashe malaman makaranta ne.

1615 GMT — An ji karar fashewar abubuwa kusa da Rafah

Rahotanni na cewa an ji karar fashewar abubuwa da kuma jiniyar motocin daukar marasa lafiya a kusa da Mashigar Rafah, tsakanin Masar da Gaza.

Fashewar na zuwa ne jim kadan bayan rukuni na biyu na manyan motoci 17 dauke da kayayyakin agaji sun tsallaka iyakar Rafah din domin shiga Gaza.

1525 GMT — Dakarun Hamas sun yi wa sojojin Isra'ila kwanton-bauna

Dakarun Hamas sun ce sun yi kwanton-bauna ga sojojin Isra’ila a gabashin birnin Khan Yunis da ke kudancin Gaza.

Dakarun na Hamas sun ce sun tilasta wa sojojin na Isra’ila ja da baya sa’annan kuma suka lalata musu buldoza biyu da tankar yaki daya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da adadin ‘yan Isra’ila da Hamas ta kashe suka kai 1,400, sa’annan wadanda ta raunata kuma suka kai 5,132.

1330 GMT — Isra'ila ta kashe 'yan jaridar Falasdinu 18

'Yan jarida akalla 18 na Falasdinu Isra'ila ta kashe a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba bayan fara yaki tsakanin Hamas da Isra’ila

Dan jarida na baya-bayan nan da aka kashe shi ne Rushdi Sarraj, wanda ya rasa ransa a hare-haren da Isra’ila take kaiwa, kamar yadda kungiyar ‘yan jarida ta Falasdinu ta bayyana a wata rubutacciyar sanarwa da ta fitar.

Har yanzu Isra’ila na ci gaba da luguden wuta a sassan Falasidinu musamman Gaza.

1205 GMT Rukuni na biyu na manyan motoci dauke da kayan agaji ya shiga Gaza

Rukunin na biyu na ayarin manyan motoci dauke da kayan agaji ya shiga Zirin Gaza, kamar yadda majiyoyin tsaro da ayyukan jin kai a Rafah suka tabbatar.

Majiyoyin sun tabbatar da cewa sai da aka yi bincike kan motocin a Mashigar Rafah kafin aka bar su suka tafi.

Jimlar motoci 17 ne aka tabbatar sun kama hanya zuwa Gaza, kamar yadda majiyoyin suka tabbatar.

1040 GMT — Indiya ta aika da tan 38 na kayayyakin agaji ga Falasdinawa

Kasar Indiya a ranar Lahadi ta aika da tan 38.5 na kayayyakin agaji ga yankin Sinai na Masar domin Falasdinawa fararen hula su amfana.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje na Indiya Arindam Bagchi ya bayyana cewa jirgin soji na India C-17 “dauke da tan 6.5 na kayayyakin lafiya da tan 32 na kayayyakin agaji ga jama’ar Falasdinu” sun kama hanyar zuwa filin jirgin El Arish na Masar.

Bagchi ya ce kayayyakin sun hada da magunguna da kayan tiyata da tenti-tenti da jakunan bacci da kayan amfani a ban-daki da sinadaren tsaftace ruwa da sauransu

0955 GMT — Jirgin Fadar Shugaban Turkiyya dauke da likitoci na hanyar zuwa Masar

Jirgin fadar shugaban Turkiyya dauke da magunguna da kayayyakin asibiti da za a kai Gaza ya kama hanyar zuwa Masar daga Ankara babban birnin Turkiyya.

Haka kuma jirgin na dauke da kwararru 20 ta fannin kiwon lafiya wadanda ake sa ran za su je Gaza domin bayar da agajin lafiya.

Ministan Lafiya na Turkiyya Fahrettin Koca ya wallafa sako a shafinsa na Twitter inda ya bayyana cewa likitocin za su je su yi bincike kan yadda za a kafa wata kwarya-kwaryar asibiti a filin jirgin El-Arish da ke Sinai da kuma a masigar Rafah

0915 GMT — An kashe Falasdinawa sama da 50 a ranar Asabar da dare

Hukumomin Lafiya a Falasdinu sun bayyana cewa sama da Falasdinawa 50 aka kashe a ranar Asabar da dare a Gaza.

Wannan na zuwa ne bayan an kashe Falasdinawa akalla 352 a Gaza a ranar Juma’ar da ta gabata.

Tun daga fara wannan yaki, an kashe Falasdinawa sama da 4,400 a Falasdinu, ciki har da dubban yara da mata.

A Isra’ila kuwa, adadin wadanda suka mutum tun bayan soma wannan yaki ya kai 1,400, kamar yadda hukumomi suka bayyana a can.

AA
AFP
Reuters