Lahadi, 18 ga August, 2024
1212 GMT — Aƙalla jami’an kare fara hula 82 Isra’ila ta kashe tare da jikkata sama da 720 a hare-haren da take kaiwa Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba.
Sojojin na Isra’ila na yawan kai hare-hare kan kan ofisoshin jami’an da motocinsu, kamar yadda sanarwar da hukumar kare farar hular ta fitar.
Hukumar ta zargi Isra’ila da kawo "cikas da gangan ga ayyukan jin kai da kare rayukan farar hula" a Gaza.
A cewar hukumar, dakarun farar hula sun yi nasarar gano gawarwakin mutum 35,000, yayin da mutane kusan 10,000 suka makale a karkashin baraguzan ginin.
0753 GMT — Aƙalla Falasɗinawa 11 sojojin Isra’ila suka kashe a ranar Lahadi a wani hari da suka kai a tsakiyar Zirin Gaza.
Majiyoyin kiwon lafiya daga asibitin Al-Aqsa sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa Isra’ilar ta kashe Falasɗinawa bakwai da jikkata wasu da dama a yayin wani hari a birnin Deir al-Balah.
Majiyoyin sun ƙara da cewa akwai ƙarin mutum huɗu da Isra’ilar ta kashe tare da raunata da dama a wani hari na daban da Isra’ilar ta kai sansanin gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Zirin Gaza.
2100 GMT — Wani harin sama da Isra'ila ta kai yankin Gaza da aka mamaye ya kashe aƙalla mutane 18, dukkansu daga gida ɗaya, sa'o'i bayan masu shiga tsakani sun bayyana kyakkyawan fatan cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Harin na jirgin sama ya afka wa wani gida da wani wajen ajiye kaya inda mutanen da suka rasa gidajensu suke samun matsuguni, a wajen shiga garin Zawaida, kamar yadda Asibitin Shahidai na Al-Aqsa a Deir al-Balah inda aka kai mutanen ya bayyana.
2255 GMT — Isra'ila ta yi da'awar an kashe mata manyan sojoji biyu a Gaza
Wani bam da ƙungiyoyin gwagwarmaya na Falasɗinawa suka ɗana a gefen hanya ya kashe manyan sojojin Isra'ila biyu a tsakiyar Gaza, a cewar sojoji.
Ɗaya daga cikinsu, jami'in mai kula da kayayyaki Manjo Yotam Itzhak Peled mai shekara 34 na "BataliyarJerusalem ta 8119 ... bam ɗin da Hamas ta dasa a gefen hanya ne ya kashe shi," a cewar rundunar sojan a cikin wata sanarwa.
A cikin wata sanarwar daban kuma, ta ce jami'i na biyu shi ne Sa Manja Mordechai Yosef Ben Shoam.
Shi ma mai shekaru 34, "direban babbar mota a BataliyarJerusalem ta 8119 ... yana cikin tawagar da suke kan hanyar kai wa sojojin Isra'ila kayayyaki a yankin Zeitoun na birnin Gaza," kamar yadda sanarwar ta bayyana.