Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a kullum waɗanda akasarinsu yara ne da mata. / Hoto: AA / Photo: AP

1109 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 42 a hare-hare biyu da ta kai Gaza

Aƙalla Falasɗinawa 42 Isra’ila ta kashe a yayin wani hari da ta kai a unguwannin Al-Tuffah da Al-Shati da ke Gaza, kamar yadda Ismail Al-Thawabta ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, wanda shi ne daraktan watsa labarai na gwamnati.

Majiyoyin kiwon lafiya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa sojojin Isra’ila sun kai hari kan wani gida a unguwar Al-Tuffah da ke gabashin Gaza, inda suka kashe Falasɗinawa 17 da jikkata da dama.

Sun bayyana cewa an kashe wasu ƙarin Falasɗinawa 24 da kuma jikkata da dama a wani bam ta Isra’ilar ta tayar a sansanin gudun hijira na Al-Shati da ke yammacin Gaza.

Shaidun ganin da ido sun tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa akwai gidaje sama da 20 a yankin waɗanda harin na Isra’ila ya lalata

0924 GMT — Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza ya haura 37,500

Akalla Falasdinawa 37,551 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai Gaza tun watan Oktoban bara, in ji ma’aikatar lafiya a yankin da aka yi wa ƙawanya.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa wasu mutane 85,911 kuma sun jikkata a harin, galibi mata da kananan yara.

"Hare-haren Isra'ila sun kashe mutum 101 tare da jikkata wasu 169 a cikin sa'o'i 24 da suka wuce," kamar yadda sanarwar ta bayyana.

2253 GMT — Hamas ta ce za ta amince da duk wani tsari da zai kawo ƙarshen yaƙin Isra'ila a Gaza

Ismail Haniyeh, shugaban ƙungiyar Hamas da ke gwagwarmayar kare Falasɗinawa, ya jaddada matsayarsu cewa ƙofarsu a buɗe take game da duk wata tattaunawa da za ta kawo ƙarshen kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza idan hakan ya dace da buƙatunsu.

Haniyeh ya bayyana haka ne a wata lacca a birnin Beirut inda aka tattauna game da hanyoyin kawo ƙarshen yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza.

Shugaban Hamas ya ce a shirye ƙungiyarsu take ta bayar da haɗin kai game da "duk wata yarjejeniya ko tsari da zai tabbatar da matsayarmu a tattaunawar tsagaita wuta."

Ya jaddada matsayar Hamas ta kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya, da janyewar Isra'ila daga yankin da sake gina shi da kai kayan agaji da kuma yin musayar fursunoni.

2030 GMT —Dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa 19, ciki har da waɗanda suka dawo daga aikin Hajji

Dakarun mamaya na Isra'ila sun sace Falasɗinawa 19 a wani samame da suka kai Gaɓar Yammacin Kogin Jordan kafin asubahi, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasɗinu WAFA, wanda ya ambato majiyoyi da dama.

Dakarun mamaya na Isra'ila sun sace Falasɗinawa 19 a wani samame da suka kai Gaɓar Yammacin Kogin Jordan kafin asubahi, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasɗinu WAFA, wanda ya ambato majiyoyi da dama.

Dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa biyu waɗanda suka dawo daga aikin Hajji a kan iyaka da Jordan, in ji WAFA. An sace sauran mutanen ne a garuruwan Tulkarm, Nablus, Yatma, da Ramallah.

An sace mutanen ne ba tare da wani sammaci ba, kuma dakarun Isra'ila sukan yi irin wannan garkuwa da Falasɗinawa a duk inda Isra'ila ta ga damar yin amfani da ƙarfin-tuwo don cin zarafin Falasɗinawa.

Sojojin Isra'ila sun sace tare da ɗaure Falasɗinawa sama da 9,500 tun daga watan Oktoban da ya gabata, idan aka kwatanta da Isra'ilawa 116 da Hamas da sauran ƙungiyoyin gwagwarmayar Falasɗinawa suke tsare da su a Gaza tun wancan lokacin.

Sojojin Isra'ila sun sace tare da ɗaure Falasɗinawa sama da 9,500 tun daga watan Oktoban da ya gabata, idan aka kwatanta da Isra'ilawa 116 da Hamas da sauran ƙungiyoyin gwagwarmayar Falasɗinawa suke tsare da su a Gaza tun wancan lokacin. / Hoto: Reuters

1930 GMT — Kashi 76 na makarantun Gaza suna buƙatar a sake gina su: UNRWA

Hukumar kula da Falasɗinawa 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya, UNRWA, ta ce kashi 76 na makarantun Gaza suna buƙatar a sake gina su baki ɗaya.

"A Gaza, fiye da kashi 76 na makarantu suna buƙatar a sake gina su idan ana so a yi amfani da su," a cewar wata sanarwa da ƙungiyar samar da ilimi ta the Global Education Cluster ta ambato UNRWA tana bayyanawa.

UNRWA ta ƙara da cewa duk da yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, tawagarta "tana ci gaba da isa ga ƙananan yara wajen koyar da su da kuma yi musu wasa," tana mai jaddada cewa "ilimi shi ne babban 'yancin da ɗan'adam yake da shi" sannan ta nanata kiran da ta yi na daina kai hare-hare a yankin.

TRT Afrika da abokan hulda