Talata, 10 ga Satumban 2024
1454 GMT –– Jami'in kula da harkokin wajen kungiyar Tarayyar Turai ya yi Allah-wadai da mummunan harin da Isra'ila ta kai kan wani yanki da ta ayyana a "tudun-mun-tsira" a kudancin Gaza, tare da yin kira da a dauki mataki.
"Dole ne a mutunta dokokin yaki, kare fararen hula da kuma tabbatar da kama mai laifi," in ji Borrell a shafin X, ya kara da cewa: "Ba za mu iya daidaita bala'in jinƙai a Gaza ba."
Akalla mutane 40 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan wani tanti da ke Khan Younis a yankin al-Mawasi, wanda Isra’ila ta ayyana a matsayin “tudun-mun-tsira” ga fararen hula da suka rasa matsugunansu a Gaza.
Ma'aikatar tsaron Gaza ta ce makamai masu linzamin na Isra'ila sun ƙona tantunan 'yan gudun hijira tare da haddasa ramuka masu zurfin mita tara a yankin.
2225 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 40 da jikkata 60 a Khan Younis
Likitoci sun ce Isra'ila ta kashe Falasdinawa akalla 40 tare da raunata wasu 60 a harin da ta kai ta sama a wani sansani da ke Khan Younis a kudancin Gaza.
Wani jami’in kare farar hula ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a safiyar Talata cewa an gano mutane “40 da suka yi shahada da 60 da aka jikkata inda aka aika da su” asibitocin da ke kusa bayan wani hari da Isra’ila ta kai Al-Mawasi da ke Khan Younis.
Mazauna da likitoci da ke sansanin sun bayyana cewa Isra’ila ta yi amfani da makamai masu linzami aƙalla huɗu.
Sansanin na cike da mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon irin munanan hare-haren da Isra’ila ta rinƙa kaiwa a Gaza.
0911 GMT –– Aƙalla jami’an kare farar hula bakwai na Falasɗinawa Isra’ila ta kashe a wani sabon harin da ta kai a Gaza.
Mutum huɗu sun rasa ransu inda wasu da dama suka jikkata bayan wani jirgin yaƙin Isra’ila ya kai hari kan wani wurin sayar da abinci a al-Shawwa da ke gabashin Gaza, kamar yadda mai magana da yawun hukumar kare farar hula Mahmoud Basal ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
Ƙarin mutum uku Isra’ila ta kashe a wani hari da ta kai birnin Rafah, kamar yadda ya ƙara da cewa.