0926 GMT — Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa goma a wasu sabbin hare-hare a Gaza
Akalla Falasdinawa 10 ne aka kashe a ranar Lahadin a wasu hare-haren da Isra’ila ta kai kan wasu yankuna a Zirin Gaza.
Wasu majiyoyin kiwon lafiya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa Falasdinawa takwas ne suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata sakamakon harin bam da Isra'ila ta kai kan wani gida da ke unguwar Al-Sabra da ke kudancin birnin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa na Wafa ya ruwaito cewa, jiragen yakin Isra’ila sun kai hari kan wasu 'yan kasar a kusa da wata tashar wutar lantarki a arewacin sansanin Nuseirat da ke tsakiyar zirin Gaza, inda suka kashe Falasdinawa biyu tare da raunata wasu.
0457 GMT —Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa biyar a yankunan fararen-hula na Gaza
Falasɗinawa aƙalla biyar sun mutu sannan da dama sun jikkata sakamakon wani hari ta sama da na makaman atilari da Isra'ila ta kai da sanyin safiya a tsakiya da yammacin Birnin Gaza.
Falasɗinawa uku sun mutu, kana wasu sun jikkata ciki har da yara da mata a harin da Isra'ila ta kai a wani gida da ke kusa da Al Jawhara Tower a tsakiyar Birnin Gaza, a cewar kamfanin dillancin labarai na WAFA.
Kazalika, jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe mutum biyu sannan sun jikata wasu a harin da suka kai a wani gida a sansanin 'yan gudun hijira na Al Shati a yammacin Birnin Gaza.
Haka kuma, Isra'ila ta yi ta luguden wuta a tsakiya da kudancin Rafah, sannan jiragen yaƙinta sun kai hari a wani gida a arewacin Rafah.
2231 GMT — Tarayyar Turai ta soki Isra'ila saboda kai hari a ofishin ICRC na Gaza, ta yi kira a yi bincike
Tarayyar Turai ta yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai a Gaza wanda ya lalata ofishin ƙungiyar bayar da agaji a International Committee of the Red Cross (ICRC), sannan ya yi sanadin mutuwar mutane.
Jami'in tsare-tsare na Tarayyar Turai Josep Borrell ya jaddada muhimmancin hukunta waɗanda ke da hannu a wannan aika-aika ta hanyar gudanar da bincike mai zaman kansa.
"Tarayyar Turai ta yi tir da yin luguden wuta da ya yi sanadin lalata ofishin ICRC a Gaza da mutuwar mutane da dama," in ji Borrell a saƙon da ya wallafa a shafin X.
"Ya kamata a gudanar da bincike mai zaman kansa kana a hukunta duk wanda ke da hannu a wannan lamari.”
Borrell ya jaddada muhimmancin kare rayukan fararen-hula, inda ya ce kare rayukansu "wajibi ne a Yarjejeniyar Geneva," wadda "duk ɓangarorin da ke rikici suka kamata su kiyaye."
2226 GMT — Masu fafutuka a London sun sha alwashin ci gaba da zanga-zanga har sai an daina 'kisan kiyashi' a Gaza
Falasɗinawa masu fafutuka sun gudanar da gangami na goyon bayan al'ummar Gaza, inda suka sha alwashin ci gaba da yin zanga-zanga har "sai an kawo ƙarshen kisan kiyashi tare da 'yartar da Falasɗinawa."
A yayin da suka taru a Lambin Victoria Embankment, masu zanga-zangar sun yi tir da gwamnatocin ƙasashen Yamma waɗanda suka yi "gum da bakunansu" a yayin da Isra'ila take ci gaba da kashe al'ummar Gaza, inda ta halaka Falasɗinawa sama da 37,500 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.
Da take jawabi a wurin gangamin, 'yar mai fafutuka mai suna Hala, wadda 'yar asalin yankin Gaza ce, ta bayyana mayuyacin halin da yankin ke ciki, inda mutane suke fama da tsananin yunwa da cututtuka.
Ta caccaki gwamnatin Birtaniya, wadda kawo yanzu ta ƙi amincewa da Falasɗinawa da aka jikkata su shiga ƙasar domin samun kulawar likitoci.
"Har yanzu da muke magana, gwamnatin Birtaniya ba ta karɓi ko da majinyaci ɗaya daga Gaza ba. Watanni takwas ke nan ana kai mana hare-hare amma ƙasar da ke iƙirarin zama ɗaya daga cikin waɗanda suka ci gaba a duniya ta ƙi bari ko da mutum ɗaya ya yi jinya...ko da mutum guda ɗaya," in ji ta, inda sauran masu zanga-zanga suka yi ihun cewa hakan "Abin kunya ne."