The Israeli army has killed 30 more Palestinians in attacks across Gaza, taking the death toll to 39,653 since October 7 last year. / Photo: AA

Talata, 6 ga watan Agusta, 2024

1121 GMT –– Isra'ila ta kai hari a garin Maifadoun da ke kudancin Lebanon inda ta kashe aƙalla mutum biyar, a cewar Ma'aikatar Kiwon Lafiyar ƙasar.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta ce ma'aikatan ceto suna can suna ƙoƙarin neman waɗanda suka tsira bayan harin da Isra'ila ta kai wani gida a garin.

A gefe guda, Isra'ila ta jikkata mutum biyu a luguden wutar a garuruwan Khiyam da Wazzani da ke kan iyaka, a cewar ma'aikatar.

0958 GMT ––Adadin Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe a yaƙin Gaza ya kai 39,653

Sojojin Isra'ila sun kashe ƙarin Falasɗinawa 30 a hare-haren da suka kai a yankuna daban-daban da ke Gaza, abin d ya sa adadin mutanen da suka kashe ya kai 39,653 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta yankin.

A wata sanarwa da ta fitar, ta ƙara da cewa mutum 91,535 sun jikkata.

"Dakarun Isra'ila sun kashe mutum 30 tare da jikkata 66 a 'kisan kiyashi' uku da suka yi a wasu gidaje a awanni 24 da suka gabata," in ji ma'aikatar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, "Mutanen da dama sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine da kan hanyoyi domin masu aikin ceto sun kasa isa wurin da suke."

Falasɗinawa suna alhinin kisan ɗan'uwansu da Isra'ila ta yi a sansanin 'yan gudun hijira na Bureij da ke Deir al-Balah, Gaza, Agusta 6, 2024. / Hoto: AA

0603 GMT —Dakarun Isra'ila sun ƙara ƙaimi wurin kai samame a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla huɗu a wani samame da suka kai da tsakar dare a garin Aqaba kusa da birnin Tubas da ke arewacin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.

A wata sanarwa da ta fitar, Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Falasɗinu ta ce an kashe Falasɗinawa aƙalla hudu tare da jikkata da mutum bakwai, biyu daga cikinsu mummunan rauni sakamakon wutar da dakarun Isra'ila suka buɗe a garin Aqaba.

Kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu Wafa ya ambato wasu majiyoyi suna cewa sojojin Isra'ila sun kai samame garin Aqaba inda suka rufe wani gida, lamarin da ya haifar da arangama da Falasɗinawa.

Ya ƙara da cewa sojojin Isra'ila sun tsare wani Bafalasɗine bayan an jikkata shi a cikin gidan da aka rufe.

Gidajen da dakarun Isra'ila suka lalata yayin da suka kai samame a garin Tulkarem na Gaɓar Yamma da Kogin Jordan ranar 3 ga watan Agusta, 2024. / Hoto: AA

2319 GMT — An yi wa Haniyeh kisan gilla ne da zummar tsawaita yaƙin Gaza — Abbas

An yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh kisan gilla ne da zummar tsawaita yaƙin Gaza da kuma dagula tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin, a cewar shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas a hira da kamfanin dillancin labaran RIA na gwamnatin Rasha.

"Babu tantama cewa an yi wa Mr. Haniyeh kisan gilla ne domin tsawaita yaƙin da kuma faɗaɗa shi," in ji Abbas, kamar yadda RIA ya ambato shi yana bayyanawa.

"Kisan nasa zai yi mummunan tasiri a kan yarjejeniyar da ake ƙoƙarin ƙullawa ta tsagaita wuta da kuma janyewar dakarun Isra'ila daga Gaza."

"Babu tantama cewa an yi wa Mr. Haniyeh kisan gilla ne domin tsawaita yaƙin da kuma faɗaɗa shi," in ji Abbas. / Hoto: AA Archive

2035 GMT — Amurka na neman a yi sulhu yayin da Iran ke shirin ramuwar gayya kan Isra'ila

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya yi kira ga Tehran da Tel Aviv su amince da tsagaita wuta Gaza domin "karya lagon yaƙin" da ke faruwa, a yayin da Iran take shirin yin ramuwar gayya kan Isra'ila.

"Ƙara aukawa cikin yaƙi ba zai yi wa kowa daɗi ba. Zai haddasa ƙarin yaƙi da tazoma da rashin tsaro. Yana da muhimmanci mu karya lagon wannan yaƙin ta hanyar amincewa da tsagaita wuta a Gaza," in ji Blinken a hira da manema labarai.

Blinken ya yi kiran ne a yayin da ake cikin zaman ɗarɗar kan yiwuwar hare-haren da Iran da ƙawayenta za su kai wa Isra'ila domin yin martani kan kisan shugaban Hamas da kwadandan Hezbollah a makonnin da suka gabata.

Shugaan Amurka Joe Biden, wanda ƙasarsa ta aike da jiragen ruwan yaƙi da manyan makakai yankin Gabas ta Tsakiya, yana shirin gudanar da taro mai muhimmanci da shugabannin tsaron ƙasarsa.

Shugaban sojojin Amurka da ke kula da Gabas ta Tsakiya, Janar Michael Kurilla, ya isa Isra'ila inda ya gana da shugaban rundunar sojin ƙasar Laftanar Janar Herzi Halevi domin tattaunawa kan shirin kare kansu, a cewar wata sanarwa da suka fitar.

Wannan hoton wanda aka ɗauka daga arewacin Isra'ila, kusa da kan iyaka da Lebanon, ya nuna yadda hayaƙi ya tirniƙe sararin samaniya bayan Isra'ila ta kai hari a yankin Wazzani na Lebanon ranar 5 ga watan Agusta, 2024. / Hoto: AFP

2123 GMT — An jikkata wasu jami'an Amurka a harin da aka kai Iraƙi

An jikkata jami'an Amurka da dama sakamakon wani harin roka da a sansaninsu da ke Iraƙi, a cewar kakakin ma'aikatar tsaron ƙasar.

"An kai harin da muke zargi na roka ne a yau a kan dakarun Amurka da abokan aikinsu a sansanin sojin sama na al-Asad da ke Iraƙi. Bayanan farko sun nuna cewa jami'an Amurka da dama sun jikkata," in ji shi.

Babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin na sansanin Ain al-Assad.

TRT Afrika da abokan hulda