Dakarun Isra'ila sun kai hari Zirin Gaza da Kudancin Lebanon kwana guda bayan an harba wa kasarsu bama-bamai da gurneti daga yankin Falasdinu da Lebanon.
An harba makaman ne a wani matsayin martani kan hare-haren da dakarun Isra’ila suka kai masallacin Kudus - wuri na uku mafi tsarki a Musulunci.
Kungiyar Hamas da ke rike da mulkin wani yanki da ke gabar tekun Gaza ta ce da safiyar Juma'a dakarun Isra'ila sun kai hare-hare da dama ta sama a yankin, amma kawo yanzu babu rahoton rasa rayuka.
"A halin yanzu dakarun sojin tsaron Isra’ila IDF na ci gaba da kai hari Gaza," a cewar IDF a shafinsu na Twitter.
Dakarun Isra'ila sun ce an ji karar harbe-harbe ta sama a kudancin kasarsu, lamarin da ya nuna cewa an sake harba sabon bam daga Gaza.
Daga baya an ji karar fashewar abubuwa akalla uku a yankin Tyre na kasar Lebanon, yayin da sojojin Isra’ila suka ce suna kai hare- hare a can.
"Akalla harsashi biyu ne suka fado" a wani sansani na 'yan gudun hijira na Falasdinawa da ke kusa da birnin Tyre, in ji Abu Ahmad wani mazaunin sansanin, wanda ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.
Ya ce "ya ji karar fashewar abubuwa".
Majiyoyi biyu na jami'an tsaron Lebanon sun ce harin ya far wa wa wani karamin gini ne da ke kan gonakin da ke kusa da yankin da aka harba rokoki a safiyar Juma'a. Sai dai ba su da rahoto ko an rasa rayuka.
A wata sanarwa ta daban, Hamas ta ce, ‘’Mun yi tir da kakkausar murya ga iri wannan aika-aika ta wuce-gona-da-iri da aka kai yankin da ke kusa da birnin Tyre na kasar Lebanon da sanyin safiya."
Abin da ya sa Masallacin Kudus ke da matukar muhimmanci ga Musulmai
Darukun Isra’ila sun ce ba za su kyale Hamas ta kai musu hare-hare daga cikin Lebanon ba sannan za su "dora wa Lebanon alhakin duk wani hari da aka kai daga yankin," a cewar sanarwar.
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da aka tura kudancin Lebanon sun yi kira ga "dukkan bangarorin biyu su dakatar da duk wani mataki" da suka dauka kan iyakoki biyun.
Turkiyya ta caccaki Isra'ila
Hare-haren na zuwa ne jim kadan bayan Firaiminista Benjamin Netanyahu ya yi alkawarin mayar da martani mai karfi kan irin rokokin da ake harba kasarsa.
"Za mu lallasa abokan gabarmu kuma za su dandana kudarsu kan duk wani harin ta'addanci," in ji Netanyahu a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin.
Sojojin Isra'ila sun ce sun "gano makaman roka 34 da aka harba daga yankin Lebanon zuwa cikin kasar Isra'ila" mafi girman hari da ya taba faruwa a yankin tun bayan yakin kwanaki 34 da Isra'ila da Hizbullah suka yi a 2006.
Sanarwar ta kara da cewa sojojin saman Isra'ila sun kama makaman roka 25, "yayin da wasu rokoki biyar suka fado yankin na Isra'ila."
Babu kungiyar da ta dauki alakin kai harin.
Turkiyya ta yi kakkausar suka ga Isra'ila, inda ta bukaci ta gaggauta kawo karshen tashe-tashen hankula da ta shafe kwanaki tana yi da gangan."
"Muna Allah wadai da hare-haren wuce-gona-da-iri da Isra'ila ke kai wa Gaza. Za mu ci gaba da tallafa wa 'yan uwanmu Falasdinawa. Wannan zaluncin zai kawo karshe!, in ji mai magana da yawun shugaban Turkiyya Ibrahim Kalin.
Shi ma Firaiministan Lebanon, Najib Mikati, ya yi tir da duk wani “tashin hanakali” da Isra'ila ta haddasa a kasarsa sakamakon harin makaman roka.