1041 GMT — Isra'ila ta ce an kashe sojojinta 250 tun fara yaƙin Gaza
Yawan sojojin Isra'ila da aka kashe a Gaza ya kai 250 tun bayan fara yaƙinta a Gaza da aka yi wa ƙawanya a farkon watan Oktoba, kamar yadda bayanan baya-bayan nan da rundunar sojin ta fitar suka nuna.
An kashe soja na 250 ɗin ne a yau Litinin a wani bayani da wata majiyar tsaro ta ce hari ne da aka kai asibitin Al Shifa, wanda shi ne mafi girma a Gaza.
1042 GMT — Sojojin Isra'ila sun kama ƴan jarida da dama a asibitin Al-Shifa da ke Gaza
Rundunar Sojin Isra’ila a ranar Litinin ta kama ƴan jarida dama a asibitin Al-Shifa da ke Zirin Gaza, kamar yadda waɗanda suka shaida lamarin suka tabbatar.
“Dakarun Isra’ila sun yi musu duka, sun rufe musu ido da ƙyalle inda suka kama su,” kamar yadda wani da ya shaida lamarin ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu. Kafar watsa labarai ta Al Jazeera ta tabbatar da kama wakilinta Ismail Al-Ghoul.
Da safiyar Litinin ne sojojin Isra’ilar suka afka wa asibitin Al-Shifa, wanda ke ɗauke da dubban marasa lafiya da kuma waɗanda aka raunata da waɗanda suka rasa muhallansu.
1042 GMT — Sojojin Isra’ila sun afka asibitin Al-Shifa da ke Gaza
Rundunar Sojin Isra’ila a ranar Litinin ta sanar da cewa dakarunta sun afka harabar Asibitin Al-Shifa wanda ke ɗauke da dubban marasa lafiya da kuma waɗanda aka raunata da waɗanda suka rasa muhallansu.
Ɗumbin Falasɗinawa aka kashe tare da raunatawa a daidai lokacind a tankokin yaƙin Isra’ila suka buɗe wuta sannan suka afka cikin yammacin na Gaza inda suka yi wa asibitin ƙawanya, kamar yadda waɗanda suka shaida lamarin suka bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
Sai dai kafar watsa labarai ta gwamnatin Isra’ila KAN ta ruwaito cewa sojojin na Isra’ila sun afka asibitin na Al-Shifa ne bayan wasu bayanan sirri sun nuna cewa mambobin Hamas suna amfani da asibitin.
KAN din ta yi iƙirarin cewa an buɗe wa sojojin na Isra’ila wuta inda suka mayar da martani.
1845 GMT — Sama da yara 13,000 Isra'ila ta kashe a Gaza - UNICEF
Hukumar kula da ƙananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da yara 13,000 aka kashe a Gaza a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa, inda ta ƙara da cewa yara da dama na fama da rashin abinci mai gina jiki kuma ba su da kuzarin yin kuka.
Dubban mutane sun jikkata ko kuma ba za mu iya tantance inda suke ba. Wataƙila sun maƙale a karkashin ɓaraguzan gine-gine ... Ba a taɓa samun yanayin da aka kashe yara da yawa haka ba a duk wani rikici a duniya," in ji Babbar Daraktar UNICEF. Catherine Russell ta shaida wa shirin "Face the Nation" na CBS News.
"Na kasance a cikin dakunan yara masu fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki, duk dakin ya yi shiru. Saboda yara da jarirai ... ba su da kuzarin yin kuka."
Russell ya ce akwai "gaggarumin ƙalubale na tsarin mulki" ga manyan motoci masu jigilar kayan abinci zuwa Gaza don ba da agaji.
1646 GMT — Netanyahu ya ce ba zai amince da yarjejeniyar zaman lafiya da za ta bar su da 'rauni' ba.
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya ce duk wata yarjejeniyar zaman lafiyar Gaza da za ta raunana Isra'ila tare da hana ta damar kare kanta daga maƙwabta masu gaba da juna, ba za a amince da ita ba.
Duk wata yarjejeniyar zaman lafiya "wadda za ta sa Isra'ila ta yi rauni da kuma kasa kare kanta" ba abin da za ta yi sai mayar da zaman lafiya baya ba a gaba ba," in ji shi yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz a yammacin Birnin Kudus, yana mai nanata cewa "dole Isra'ila ta samu duk wani tsaro da ya wajaba".
Netanyahu ya ce Isra'ila ba za ta bar fararen hula da suka maƙale a Rafah ba lokacin da dakarunta suka fara kai farmakin da aka daɗe ana tsammanin kai wa kudancin Gaza inda Falasdinawa sama da miliyan ɗaya suka samu mafaka.
"Ba wani abu ne muke yi ba yayin da ake kulle jama'a. Maganar gaskiya ma ita ce za mu yi akasin haka, za mu ba su damar ficewa."