Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya bayyana damuwa kan yadda Isra’ila ke fadada matakan da take dauka na soja, yana gargadin cewa Isra’ila “ba za ta tsaya a Gaza ba, za ma ta shiga Lebanon.”
Gwamnatin Isra’ila da Firaminista Benjamin Netanyahu suna so ya kunna wutar yaƙi a gaba ɗaya yankin, a cewar Fidan yayin wata tattaunawa ta musamman da TRT Haber.
Ministan na harkokin ƙasashen waje ya kuma bayyana damuwa kan matakan Isra’ila na tilasta wa kawayenta shiga yaƙin, yana cewa “Isra’ila tana saka kanta da ƙawayenta a cikin wani gagarumin yaki.”
Ya caccaki irin tallafin da Amurka ke bai wa Isra’ila, yana bayyana shi a matsayin abin damuwa ne cewa, “Isra’ila na yin abin da ta ga dama da ƙarfin da Amurka ke da shi.”
Bin hanyar zaman lafiya mai ma’ana
Fidan ya kuma jadda buƙatar kafa ƙFalasdinu mai cin gashin kanta, yana nuni a kan yunƙurin da Ƙungiyar Tunutuɓa kan Gaza ke yi a yanzu haka don nuna muhimmanin lamarin.
Ya kuma jaddada rashin taɓukawar Majalisar Ɗinkin Duniya wajen magance wahalhalun da mutane ke sha a Gaza, inda ya ce tsarin MDD ya kasa ɗaukar matakin da ya dace.
Duk da yadda yaƙin ke ƙara faɗaɗa, Fidan ya jaddada ƙudirin Turkiyya wajen bin hanyar zaman lafiya mai ma’ana a yankin, yana mai jaddada muhimmaincin matsayar Shugaba Erdogan ta diplomasiyya kan lamarin.
Akalla mutane 11 aka kashe aka kuma jikkata wasu108 a hare-haren da Isra’ila ta kai tun ranar Juma’a, abin da ya kai yawan mutanen da suka mutu tun ranar 16 ga Satumba zuwa 1,030, aka kuma jikkata 6,352, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta bayyana.
An kuma raba fiye da mutue 200,000 da gidajensu a cikin Lebanon saboda hare-haren Isra’ila, a cewar babban kwamishinan hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya.