Laraba, 31 ga watan Yuli, 2024
1352 GMT — Iran ta kira kisan gillar da aka yi wa Haniyeh "wani sabon bayyanannen ta'addancin gwamnatin Isra'ila"
Mataimakin shugaban ƙasar Iran Mohammad Reza Aref ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa shugaban siyasa na Isra'ila Ismail Haniye, yana mai cewa "wani sabon bayyanannen ta'addancin gwamnatin Isra'ila"
Aref ya ce kisan gilar Haniyeh na ɗaya daga cikin munanan sakamakon shirun d aƙsashen duniya ke yi kan ci gaba da aikata munanan laifuka da gwamnatin masu tsattsauran ra'ayin kafa ƙasar isra'la ke yi da kuma take dokokin ƙsa da ƙasa muraran.
1214 GMT — Falasɗinawa sun yi zanga-zanga bayan yi wa Haniyeh kisan gilla
Falasɗinawa sun gudanar da zanga-zanga a faɗin Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye don yin Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa shugaban siyasa na ƙungiyar Hamas, Ismail Haniyeh a Tehran.
Masu zanga-zangar sun yi ta ɗaga tutoci da kwalayen Hamas a yayin da suke maci a birnin Ramallah suna ihun nuna goyon bayan ƙungiyoyin gwagwarmayarsu da nuna adawa da mamayar Isra’ila, kamar yadda wani ɗan jarida na kamfanin dillancin laraban Turkiyya Anadolu ya faɗa.
An kuma yi wasu jerin zanga-zangar a sauran biranen da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan da suka haɗa da Hebron da Bethlehem da Nablus da Jenin da Tulkarem da Tubas da kuma Qalqilya.
0949 GMT — Za a binne shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Doha ranar Juma'a kwana ɗaya bayan an yi masa jana'iza a Tehran, a cewar wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar.
Hamas ta ce za a yi jana'izar "ban-girma kuma a bainar jama'a" a Tehran ranar Alhamis sannan daga bisani a kai gawarsa Doha ranar Juma'a domin binne "shugaban wanda ya yi shahada".
1055 GMT — Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza ya kai 39,445
Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa aƙalla 45 a hare-haren da ta kai Gaza, lamarin da ya sa adadin waɗanda ta kashe a yankin ya kai 39,445 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar Ma'aikatar Kiwon lafiya ta Gaza.
Ma'aikatar ta ƙara da cewa hare-haren sun jikkata mutum 91,073.
"Dakarun Isra'ila sun kashe mutum 45 tare da jikkata mutum 77 a awowi 24 da suka gabata sakamakon hare-hare babu ƙaƙƙautawa a Gaza," in ji ma'aikatar.
Ta ƙara da cewa, "Mutane da dama suna danne a ƙarƙashin ɓaraguzai da kuma kan hanyoyi saboda masu aikin ceto sun kasa isa inda suke".
0811 GMT — Za mu mayar da 'zazzafan martani' kan kisan gillar da aka yi wa Haniyeh: Qassam
Ɓangaren soji na Hamas ya ce kisan da aka yi wa shugaban 'ƙungiyar, Ismail Haniyeh, ya buɗe "sabon babi" a yaƙin da suke yi da Isra'ila, inda ya yi gargaɗi game da tasirin hakan kan ɗaukacin yankin.
"Wannan kisan gillar... ya buɗe sabon babi kuma zai yi mummunan tasiri ga ɗaukacin yankin," in ji Qassam Brigades, wadda mayaƙanta suke fafatawa mai zafi da dakarun Isra'ila a Gaza.
0344 GMT — Hamas ta sha alwashin ɗaukar mataki kan kisangilla da aka yi wa Haniyeh
Hamas ta ce kisan da aka yi wa shugabanta Ismail Haniyeh "babbar taƙalar faɗa ce."
Gidan Talbijin na Al-Aqsa ya ambato wani babban jami'i na ƙungiyar Hamas Moussa Abu Marzouk yana cewa kisan da aka yi wa Hamas na "matsorata ne da ba za a kawar da kai ba tare da martani ba."
Hamas da rundunar zaratan sojojin Iran ta Revolutionary Guard sun tabbatar da kisan Haniyeh a samamen da aka kai a gidansa da ke Iran, inda Hamas ta ce Isra'ila ce ta kai harin a gidansa da ke Tehran.
2107 GMT — Isra'ila ta yi iƙirarin kashe wani babban "na hannun-daman" shugaban Hezbollah Nasrallah
Rundunar sojin Isra'ila ta ce jiragen yaƙinta sun kashe "babban kwamandan soji" na ƙungiyar Hezbollah kuma shugaban ɓangaren tsare-tsarenta, Fuad Shukr, wanda aka fi sani da "Sayyid Muhsin," a harin da suka kai Beirut.
Kawo yanzu ba a tabbatar da iƙirarin da mahukunta a Tel Aviv suka yi ba.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce harin da Isra'ila ta kai Lebanon ya kashe fararen-hula uku ciki har da yara biyu.
Wata sanarwa da Isra'ila ta fitar ta ce Fuad ne na "hannun-damar" shugaban ƙungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah kuma shi ne yake ba shi shawara kan tsare-tsaren yaƙi.
"Fuad Shukr ne ya bayar da umarni ga Hezbollah don kai hari a Isra'ila ranar 8 ga watan Oktoba," a cewar sanarwar, tana mai ƙarawa da cewa shi ke da alhakin kisan yara 12 a harin da aka kai a Majdal Shams da ke yankin Tuddan Golan da Isra'ila ta mamaye.
Hezbollah ta musanta hannu a harin. Ta ce Shukr ya tsallake rijiya da baya a harin da Isra'ila ta kai.
2109 GMT — An kai hari hedkwatar ƙungiyar Hashd al-Shaabi a Iraƙi
An kai hari a hedkwatar ƙungiyar Hashd al-Shaabi a lardin Babil da ke Iraƙi, a cewar kafofin watsa labarai na ƙasar.
Harin ta sama ya sauka a hedkwatar ƙungiyar da ke garin Jurf al-Sakhar, in ji wasu rahotanni daga kafofin watsa labaran Iraƙi.
An zargi Amurka da hannu a kai harin, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu mutane tare da jikkata wasu.