Hezbollah says it attacked a new Israeli military reconnaissance command centre in Arab Al Aramshe. / Photo: AFP Archive

1216 GMT — Hezbollah ta kai hari kan sansanin Isra'ila a matsayin ramuwar gayya

Kungiyar Hezbollah ta kasar Labanon da ke samun goyon bayan Iran ta ce ta ƙaddamar da wani hari da makami mai linzami da jirage marasa matuka kan wani sansanin Isra'ila a matsayin martani ga harin da aka kashe mambobinta uku a jiya.

Hezbollah ta ce ta kaddamar da wani hari tare da makami mai linzami da bama-bamai da bama-bamai a wata sabuwar cibiyar binciken soji da ke Arab Al Aramshe, wani ƙauye da Larabawa suka fi rinjaye a arewacin Isra'ila.

Harin ya zo ne "a matsayin mayar da martani ga maƙiya da suka kashe wasu 'yan kungiyar a Ain Baal da Shehabiya a ranar Talata," in ji kungiyar.

1021 GMT — Isra'ila na fuskantar matsin lamba kan ta guji kai wa Iran hari

Isra'ila tana fuskantari matsin lamba daga ƙawayenta kan ta guji kai wa Iran hari bayan harin makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da ba a taba ganin irinsa ba da Iran ɗin ta kai wa Isra'ila, a daidai lokacin da Washington da Brussels suka sha alwashin ƙara sanya takunkumai kan Tehran.

Isra'ila na fuskantar matsin lamba kan ta guji kai wa Iran hari

Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya David Cameron da takwaransa na Jamus Annalena Baerbock su ne jakadun Ƙasashen Yammacin Duniya na farko da suka kai ziyara Isra'ila tare da yin kira da a kwantar da hankula bayan harin da Iran ta kai a karshen mako, inda Isra'ila ta sha alwashin mayar da martani.

Cameron ya ce: "Muna matukar damuwa don kauce wa ta'azzara, kuma mu ce wa abokanmu a Isra'ila: lokaci ne da za mu yi tunani da kyau kuma ta hanyoyi da dama, saboda ta ko ina aka duba wannan abu samun nasara ne a kan Iran.

Ba wai kawai harin nasu ya kasance kusan gazawa ba, har ma sauran kasashen duniya na iya ganin irin mummunar tasirin da suke da shi a yankin," kamar yadda Cameron ya shaida wa Times Radio.

0000 GMT — Rashin hankalin da Isra'ila take yi na kai wa fararen-hulan Gaza hari ya nuna gazawar sojojinta — Hamas

Ƙungiyar Hamas ta ce "haukan da masu ra'ayin Yahudanci" suke yi na kai hari a kan Falasɗinawa fararen-hula a Gaza na nuna gazawar rundunar sojin Isra'ila a yayin da ake yi mata turjiya.

"Haukan da masu ra'ayin Yahudanci suke yi a kan fararen-hula alamomi ne na gazawar sojojin mamaya kwata-kwata a yayin da suke fuskantar turjiya,'' in ji shugaban Hamas Izzat al Rishq a sanarwar da ya watsa a shafin Telegram.

Ya ƙara da cewa "Hotunan da aka ɗauka a Asibitin Shifa da ke Birnin Gaza sun nuna sojojin mamaya na ƴan Nazi suna yin kisan ƙare-dangi mafi muni a duniya a ɓangaren kiwon lafiya.''

Ya ƙara da cewa, “Goyon bayan da Amurka da ƙasashen Yamma suke bai wa haukan da masu ra'ayin Yahudanci suke yi bai sauya ba wajen faɗaɗa rikici a wannan yankin."

2100 GMT —Isra'ila ta kashe ƙarin gomman Falasɗinawa a sabbin hare-haren da ta kai Gaza

Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 28, cikinsu har da ƙananan yara da dama, a sabbin hare-hare da ta kai wurare daban-daban a yankin Gaza da ta mamaye, kamar yadda ganau suka shaida wa TRT World da kafafen watsa labaran yankin.

Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe mutum takwas a yankin Tuffah bayan sun kai hari kan wata motar ƴan sanda. Kazalika luguden wutar da Isra'ila ta yi a sansanin al-Maghazi da ke yankin Deir al-Balah na Gaza ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 13.

Haka kuma Isra'ila ta kashe Falasɗinawa bakwai a harin da ta kai wa wasu iyalai a sansanin Yabna da ke birnin Rafah. Ta jikkata mutane da dama a harin.

Wani mutum ɗauke da gawar ɗansa da ya karɓo daga Asibitin al-Aqsa Martyrs bayan harin da Isra'ila ta kai a sansanin Maghazi da ke Deir al-Balah / Hoto: AA
TRT Afrika da abokan hulda