1406 GMT — Adadin Falasdinawan da aka kashe a Gabar Yamma da Kogin Jordan ya kai 288
Bayan kashe wani matashi da sojojin Isra’ila suka yi, adadin Falasdinawan da aka kashe a Gabar Yamma da Kogin Jordan ya kai 288 tun daga 7 ga watan Oktoba, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta tabbatar a ranar Asabar.
Ma’aikatar ta sanar da hakan a wata takaitacciyar sanarwa da ta fitar kan cewa an kashe Hamza Ibrahim Muhammad Bashkar mai shekara 30 a garin Huwara a ranar Juma’a.
Duk da cewa ma’aikatar ba ta bayyana yadda aka kashe shi ba, amma wani da ya shaida lamarin daga birnin Nablus ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa sojojin sun kashe shi ne kan zargin cewa matashin ya yi kokarin caka wa daya daga cikin sojojin wuka.
1055 GMT — Falasdinawa sun koma binne iyalansu a gefen titi da asibitoci da filayen makarantu
Falasdinawa da dama na binne iyalansu da suka rasu sakamakon hare-haren sojojin Isra’ila a gefen titi da asibitoci da wuraren wasan yara.
Hakan ya faru ne sakamakon irin wahalar da Falasdinawan ke sha kafin zuwa makabartu domin binne ‘yan uwansu.
Falasdinawan da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya tattauna da su sun shaida cewa kabururan za su kasance na wucin gadi har zuwa lokacin da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, inda suka ce idan an samu hakan sai su mayar da gawarwakin zuwa makabartu.
Shugaban kungiyar kare hakkin bil adama ta Euro-Mediterranean Observatory for Human Rights, Rami Abdu ya bayyana cewa jami’ansa sun gano kaburbura na gefen titi sama da 120 wadanda aka binne mutane da dama a ciki.
1000 GMT — Hezbollah ta ce ta halaka sojojin Isra'ila da dama a wani hari kan sansaninsu
Kungiyar Hezbollah ta Lebanon a ranar Asabar ta ce ta kai hari kan sansanin sojin Isra’ila na Birket Rishe da ke kan iyakar kasar Lebanon da Isra’ila inda ta ce ta halaka sojojin da dama da raunata wasu.
Kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar inda ta ce ta yi amfani da makamai mai linzami wurin kai harin.
Rikici tsakanin Hezbollah da kuma sojojin Isra’ila ya kara kazanta tun bayan da yaki ya rincabe tsakanin sojojin Isra’ila da dakarun Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba.
0930 GMT — Dakarun Isra'ila sun raunata Falasdinawa biyar a Gabar Yamma da Kogin Jordan
Dakarun Isra’ila sun raunata Falasdinawa biyar, daga ciki har da yaro karami a biranen da ke fadin Gabar Yamma da Kogin Jordan, kamar yadda hukumomin Falasdinu suka tabbatar.
Kungiyar bayar da agaji ta Palestinian Red Crescent ta bayyana ma’aikatanta sun shiga lamarin bayan da sojojin Isra’ila suka raunata mutum biyar a Bethlehem da Hebron da Nablus.
Ta bayyana cewa akwai Falasdinawa uku da aka harba da bindiga sannan mutum biyu suka samu rauni sakamakon harin.
0900 GMT — An dakatar da 'yan sandan Isra'ila biyu kan kai wa dan jaridar Turkiyya hari
Rundunar ‘yan sandan Isra’ila ta dauki mataki domin hukunta jami’anta biyu wadanda suka kai hari kan dan jarida mai daukar hoto na kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
Kafar watsa labarai ta Channel 12 ta Isra’ila ta ruwaito cewa an dakatar da ‘yan sandan daga aiki tun bayan lamarin.
‘Yan sandan sun kai wa dan jaridar hari ne a Alkharouf a lokacin da yake daukar rahoto a wurin Sallar Juma’a kusa da Masallacin Al Aqsa da ke Gabashin Birnin Kudus.
Rahoton ya ce matakin da aka dauka kan ‘yan sandan zai ci gaba har zuwa lokacin da za a kammala bincike.