Henry Kissinger, wanda ya lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya mai cike da ce-ce-ku-ce, masanin diflomasiyya wanda ayyukansa a karkashin shugabannin kasa biyu suka jawo taɓarɓarewar manufofin harkokin wajen Amurka, ya mutu yana da shekara 100, a cewar wata sanarwa daga kamfanin Kissinger Associates Inc.
Ya mutu ne a gidansa da ke Connecticut a ranar Laraba.
Kissinger ya kasance mai kazar-kazar cikin hidima a shekarun rayuwarsa, inda ya halarci taruka a Fadar White House, ya buga littafi kan salon shugabanci, da kuma ba da shaida a gaban kwamitin Majalisar Dattawan Amurka game da barazanar nukiliyar da Koriya ta Arewa ke yi.
A watan Yulin shekarar 2023 ya kai ziyarar ba-zata a birnin Beijing domin ganawa da shugaban kasar China Xi Jinping.
A cikin shekarun 1970, ya saka hannunsa a yawancin abubuwan da suka sauya duniya na tsawon shekaru goma, yayin da yake aiki a matsayin Sakataren Harkokin Waje a karkashin shugaban ƙasa ɗan jam'iyyar Republican, Richard Nixon.
Kokarin Kissinger, wanda Bayahude ne haifaffen Jamus kuma ɗan gudun hijira, ya kai ga bude kasar China ta hanyar diflomasiyya, da muhimmiyar tattaunawa kan batun mallakar makamai tsakanin Amurka da Tarayyar Sobiyet, da faɗaɗa alaƙa tsakanin Isra’ila da maƙwabtanta na Larabawa, da yarjejeniyar zaman lafiya ta Paris da Arewacin Vietnam.
Zamanin Kissinger a matsayin mai tsara wa Amurka manufofin ƙasashen waje ya kawo ƙarshe ne a lokacin da Shugaba Nixon ya yi murabus a shekarar 1974.
Duk da haka, ya ci gaba da zama jami'in diflomasiyya a karkashin Shugaba Gerald Ford kuma yana samar da mafita mai ƙarfi a duk tsawon rayuwarsa.
Yayin da mutane da yawa ke yaba wa Kissinger saboda hazaƙarsa da kuma gogewarsa, wasu kuma sun yi masa tambari da mai aikata laifin yaƙi saboda goyon bayansa ga mulkin kama-karya na kwaminisanci, musamman a yankin Latin Amurka.
A cikin shekarunsa na ƙarshe-ƙarshe, a lokutan tafiye-tafiyensa, ya dinga cin karo da yunƙurin da wasu ƙasashe suka yi na kama shi ko kuma yi masa tambayoyi game da manufofin harkokin wajen Amurka da suka gabata.
Kyautar zaman lafiya ta Nobel ta shekarar 1973 - wadda aka ba shi tare da Le Duc Tho na Arewacin Vietnam, da ya ƙi karɓarta - na ɗaya daga cikin wadda ta jawo ce-ce-ku-ce da ba a taɓa samu ba.
Mambobi biyu na kwamitin ba da kyautar ta Nobel sun yi murabus saboda zaɓen da kuma tayar da tambayoyi game da harin bam a asirce na Amurka a Cambodia.