Baya ga yaran da suka rasu, an kuma raunata wasu mutum biyu, ɗaya daga cikinsu mace ce. / Hoto: Reuters

Aƙalla yara bakwai ne suka rasu a lardin Daraa da ke kudancin Syria bayan wani bam ya fashe, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na SANA ya ruwaito.

Wani ɗan sanda ya shaida wa kamfanin dillancin labaran cewa yara bakwai sun rasu “an kuma raunata wasu mutum biyu, ɗaya daga cikinsu mace ce, a lokacin da ƴan ta’adda suka saka tayar da bam” a birnin Sanamayn a ranar Asabar.

A rahoton da ta fitar, SANA ta ɗora alhakin kai harin kan ƴan bindiga, waɗanda suke kai hare-hare a yankin. Sai dai babu wani ƙarin bayani dangane da hakan.

Lardin Daraa ya kasance matattarar da aka kitsa bore ga Shugaba Bashar al Asaad, sai dai gwamnati ta ƙwace iko da lardin tun a 2018 bayan da aka cimma yarejeniyar tsagaita wuta wadda Rasha ta jagoranta.

Tun daga lokacin ne lardin ke fama da kashe-kashe da fadace-fadace da kuma munanan yanayin rayuwa.

Yakin Syria da ya rikide zuwa kazamin rikici wanda ya janyo masu riƙe da makamai da sojojin kasashen waje, ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 507,000 tare da raba miliyoyi da muhallansu da lalata ababen more rayuwa da masana’antu na kasar.

TRT World