Gwamnatin sojin Myanmar ta  kama Musulman Rohingya 150 da ke kokarin yin gudun hijira

Gwamnatin sojin Myanmar ta  kama Musulman Rohingya 150 da ke kokarin yin gudun hijira

Sojojin kasar sun ce sun kama 'yan Rohingyar a lokacin da suke kokarin guduwa zuwa kasar Malaysia.
Daga cikin wadanda aka kama, maza 127 ne sai kuma mata 18. Hoto/AP

Hukumomi a Myanmar sun kama kusan mutum 150 ‘yan Rohingya wadanda ake zargin suna kokarin guduwa daga kasar, kamar yadda hukumomi suka tabbatar. Ana yawan yi wa Musulman Rohingya kallon bakin haure daga Bangladesh.

An ki ba su shaidar zama ‘yan kasa haka kuma suna bukatar izini kafin su yi tafiya.

Sojoji sun kaddamar da samame kan ‘yan Rohingya a 2017, kuma dubbai a halin yanzu suna kasada da rayuwarsu domin balaguro daga sansanoni a Bangladesh da Myanmar domin tafiya wurin Musulmi da ke Malaysia da Idonesia.

An kama maza ‘yan Rohingya 127 da kuma mata 18 a ranar Juma’a kusa da kauyen Waekhamu a kudancin Jihar Mon, kamar yadda hukumomin kasar suka ce a ranar Talata.

“An kama su tun a lokacin kuma ana bincike a kansu kamar yadda dokar shige da fice ta tanada,” Aung Myat Kyaw Sein, mai magana da yawun gudanarwar Jihar Mon, kamar yadda AFP ta ruwaito.

Majalisar Dinkin Duniya a Myanmar na fuskantar zarge-zargen kisan kiyashi bayan wani samame da aka kai musu a 2017, lamarin da ya tilasta wa dubu daruruwansu tafiya Bangladesh.

A makon da ya gabata, wani jirgin ruwa dauke da ‘yan Rohingya ya samu lalace a kusa da tekun Myanmar.

Masu aikin ceto sun gano gawarwaki 17 amma sauran ba a gansu ba.

Bangladesh da Myanmar sun tattauna kan yunkurin son tasa keyar ‘yan kabilar Rohingya, duk da cewa manyan jami’an Amurka a watan da ya gabata sun ce akwai hatsari a dawowarsu.

AFP