Ginshikin da ya rike gadar Sairang wacce ke garin Aizawal na babban birnin jihar Mizoram a kasar Indiya ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama sakamokon karyewa da ta yi :Hoto Twitter/Zoramthanga

Wani bangare na gadar layin dogo da ake ginawa a jihar Mizoram ta kasar Indiya ya ruguje, lamarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 26 tare da jikkata mutum biyu, a cewar wani jami’i.

Karfe da ke kan gadar na garin Sairang da ke wajen babban birnin Aizawal ya karye ne a ranar Laraba, kamar yadda sashen kula da bayanai na ‘yan sanda ya bayyana.

An kwashe kusan shekaru biyu ana gina gadar.

Karamin Ministan sufuri na kasar TJ Lalnuntluanga, wanda ya kai ziyara wurin, ya ce an soma gano gawarwakin mutum 18 yayin da aka gano karin gawarwakin mutum takwas kuma masu aikin ceto na ci gaba da kokarin ciro wasu daga baraguzan kasa.

''Gadar layin dogo ta jirgin kasa da ake kan ginawa a Sairang da ke kusa da birnin Aizawl ta karye a yau, kuma akalla ma’aikata 15 ne suka mutu,'' a cewar babban Ministan Mizoram Zaranthang.

Bidiyon da Zoramthanga ya watsa ya nuna yadda karfen da ya karye a gadar ya fado kasa.

Mutanen da ke zaune kusa da wurin sun taimaka wajen ceto ma’aikatan da suka samu rauni an kuma wuce da su asibiti, kazalika jami’an hukumar jinkai ta tarayya sun garzaya wurin don aikin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

Tuni dai hukumomin sufuri jiragen kasa suka soma bincike kan musabbabin rugujewar gadar.

‘Yan sanda sun ce akwai ma’aikata 40 a wurin lokacin da hadarin ya afku.

Firaiministan Indiya Narendra Modi, wanda ke halartar taron BRICS a Afirka ta Kudu, ya ce ya ji takaicin afkuwar lamarin a jihar Mizoram.

"Ana ci gaba da ayyukan ceto a wurin sannan an dauki dukkan matakai don taimakawa wadanda abin ya shafa," a cewar sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Jihar Mizoram tana yankin gabas mai nisa da Indiya, sannan tana iyaka da kasar Myanmar.

TRT World