Sojoji da ma'aikatan kashe gobara sun yi ta kokarin kai wadanda suka jikkata asibitoci domin ceto rayukansu, bayan gobara ta tashi a zauren bikin aure a Hamdaniyah da ke Iraki ranar 27 ga watan Satumba, 2023. / Hoto: AFP

Akalla mutum 113 sun mutu sannan fiye da mutum 150 sun jikkata sakamakon wata mummunar gobara da ta tashi a wani wajen walimar aure a lardin Nineveh da ke arewacin Iraki, a cewar jami'an bayar da agajin gaggawa da hukumomin kiwon lafiya.

Mataimakin gwamnan Nineveh Hassan al-Allaq ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an tabbatar da mutuwar mutum 113 kawo yanzu.

An bayar da rahoton tashin gobarar ranar Talata da misalin karfe 10:45 na dare a agogon kasar.

Gwamnan lardin Nineveh, Najim al Jubouri, ya ce an yi gaggawar kai wadanda suka jikkata asibitocin lardin. Ya ce har yanzu babu takamaiman adadin mutanen da suka mutu sakamakon gobarar, abin da ke nuna cewa adadin zai iya karuwa.

Ganau sun ce wani bangare na ginin ne ya kama da wuta kuma daruruwan mutane sun halarci wurin shagalin bikin.

Bidiyoyi da hotunan da aka rika nunawa a talbijin da wallafawa a soshiyal midiya sun nuna yadda ginin ya kone kurmus yayin da mutane suke ta ihu suna kiran 'yan kwana-kwana.

Mutane sun rika ihu suna neman dauki daga wurin ma'aikatan agaji a yayin da ginin da ke lardin Nineveh yake ci da wuta./Hoto: AFP

Kawo yanzu ba a san abin da ya haddasa gobarar ba.

Sai dai bayanai sun nuna cewa wani wasan tartsatsin wuta ne ya haddasa gobarar bayan wutar ta kama a wasu sassan ginin, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Iraqi News Agency [INA] ya ambato ma'aikatar tsaron kasar tana cewa a shafinta na Telegram.

Ta kara da cewa an kewaye zauren bikin da wasu abubuwa da ke saurin daukar wuta.

Firaiministan Iraki Mohammed Shia al Sudani ya bayar da umarnin tura tawaga daga Bagadaza da sauran larduna domin taimakon ma'aikatan bayar da agajin gaggawa a wurin da lamarin ya faru.

TRT Afrika da abokan hulda