Musulmai mabiya Shi'a sun taru a cikin tsananin rana gabanin ranar Ashura a Karbala. / Photo: Reuters

Wata gobara da ta tashi a wani wajen ibada da ke birnin Karbala na Iraki ta yi sanadin mutuwar mutum hudu, a lokacin da dubban mutane suka taru don tunawa da ranar Ashura, a cewar hukumar ba da agajin gaggawa.

Wutar ta kama ne a wani dan lungu da ke kusa da kabarin Sayyadina Hussaini a ranar Juma'a, inda nan ne wajen da ake taruwa don tuna ranar.

"Binciken farko ya nuna cewa wutar ta tashi ne sakamakon fashewar wata kwalbar gas a wani kicin da aka kafa na wucin-gadi" inda mahalarta taron ke sayen abin taba- ka-lashe, daga nan sai wutar ta yadu zuwa wata kasuwa da ke daura da wajen, a cewar sanarwar hukumar ba da agajin.

'Yan kwana-kwana sun isa wajen kuma sun kashe gobarar "wacce ba ta taba faruwa ba", duk da irin kalubalen da aka fuskanta na shigar da motocinsu cikin tsukin wajen da ke cike da cincirindon mutane," sanarwar ta kara da cewa.

Tunawa da Ranar Ashura

Ashura rana ce da Sayyadina Hussaini jikan Manzon Allah SAW ya yi shahada a wani yaki da aka yi a karni na bakwai.

A ranar Asabar ne za a yi gagarumin taron tunawa da ranar ta Ashura a Karbala da Iraki in da ake sa ran dubban mutane za su halarci wajen ibadar don nuna soyayyarsu ga Sayyadina Hussaini musamman kan abin da ya faru da shi a wajen yakin a ranar.

TRT World