Wasu masu masu zanga-zanga biyu a ranar Litinin din nan sun kona Alkur’ani Mai Tsarki a gaban ofishin jakadancin Iraki da ke Copenhagen babban birnin Denmark, lamarin da ke kara dagula alakar kasashen biyu.
Masu zanga-zangar mambobin wata kungiya da ke kiran kanta “Masu Kishin Denmark” (Danish Patriot), a makon jiya suka gudanar da irin wannan zanga-zanga tare da yada ta kai-tsaye a shafin Facebook.
Wanda ya shirya zanga-zangar ta ranar Litinin a Copenhangen ya kona Alkur’ani a kusa da wata tutar Iraki da aka yasar a kasa.
Bayan afkuwar lamarin, Iraki ta la’anci wannan abu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya rawaito ma’aikatar harkokin waje na fada.
Ma’aikatar ta yi kira ga mahukuntan kasashe mambobin Tarayyar Turai da su yi gaggawar yin duba ga batun ‘yancin bayyana ra’ayi a kasashensu.
A ranar Asabar dubban ‘yan kasar Iraki sun yi zanga-zanga a babban birnin Bagadaza don nuna adawa da kona Alkur’ani Mai Tsarki da aka yi a kasashen Nordic.
Shugaban Addini na Iran Ali Khamenei a ranar Asabar ya bayyana ce wa mutanen da suka wulakanta Alkur’ani sun cancanci fuskantar hukunci mai tsanani.