Jordan, Oman da Saudiyya sun yi gargadi game da yadda ake yawan kona Alkur'ani a Denmark, sannan suka bukaci birnin Copenhagen ya dauki matakai na hana ci gaba da aiwatar da irin wannan danyen-aiki.
Ranar Asabar Jordan ta yi kakkausan suka bayan mambobin wata kungiya mai tsattauran ra'ayi sun kona Alkur'ani a babban birnin Denmark, inda ta bayya hakan a matsayin "kiyayya ga Musulunci."
A wata sanarwa, Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah wadai da wannan aiki na rashin hankali wanda ke tunzura Musulmai da nuna kiyayya da kuma yin kafar-ungulu ga zaman lafiya.
Ta jaddada cewa kona Alkura'ani mai tsarki nuna kiyayya ce zalla ga Musulunci da rashin mutunci da rashin mutunta addini, sannan ta yi kira ga kasashen duniya su dauki mataki na hakika a kan batun.
Kazalika ma'aikatar harkokin wajen ta yi kira a yi dokar da za ta hukunta masu yin wannan rashin hankali, sannan ta rika jaddada bukatar zaman lafiya da "amincewa da wadanda ba ku da ra'ayi iri daya" da hana tsattsauran ra'ayi.
Ita ma kasar Oman ta yi tir da kona littafin mai tsarki a babban birnin Denmark, tana mai bayyana hakan a matsayin yunkurin tunzura jama'a su tayar da rikici da kuma nuna kiyayya.
A wata sanarwa da ta fitar, Oman ta nemi kasashen duniya su "kalli irin wadannan matakai da ke cin fuska ga mabiya addinai da jefa kiyayya da gaba" a matsayin babban laifi.
Hukunta masu kona Alkur'ani
A wata sanarwa ta daban, Saudiyya ta yi Allah wadai da kona Alkur'ani a Denmark sannan ta nemi hukumomin kasar su dauki kwararan matakai na hana ci gaba da cin fuskar Musulmai.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar da sanarwa inda ta yi kassausan suka ga wannan mataki da ta bayyana a matsayin wanda ke tunzura mutane su yi rikici da kuma nuna kiyayya a tsakanin addinai.
Ta yi gargadin cewa sake yin wannan mummunan aiki zai sa Musulmai su kare kansu.
A ranar Juma'a ne mambobin wata kungiyar makiya Musulunci mai suna Danske Patrioter suka kona Alkur'ani mai tsarki a gaban ofishin jakadancin Iraki da ke birnin Copenhagen bayan 'yan sanda sun ba su kariya.
'Yan kungiyar sun ce sun dauki matakin ne domin mayar da martani ga harin da aka kai a ofishin jakadancin Sweden da ke birnin Bagadaza.
Ranar Alhamis da sassafe, dandazon masu zanga-zanga a Iraki sun cinna wuta a ofishin jakadancin Sweden da ke Bagadaza don nuna fushinsu ga kona Alkur'ani da wani mutum mai suna Salwan Momika ya yi a Sweden ranar 28 ga watan Yuni daidai lokacin da ake bukukuwan Sallar Layya.