Mahukunta a Iraki sun umarci jakadan Sweden da ke kasar ya tattara kayansa ya fice daga cikinta sannan suka janye jakadansu da ke Stockholm don nuna kyama ga matakin kona Alkur'ani mai tsarki.
Firaiminista Mohamed Shia al-Sudani ya "bayar da umarni ga jakadan Sweden a Bagadaza ya fice daga Iraki," a cewar wata sanara da ta fito daga ofishinsa.
An dauki matakin ne "saboda yadda gwamnatin Sweden take ci gaba da bayar da izinin kona Alkur'ani, da cin mutuncin Musulunci da kuma kona tutar Iraki".
Lamarin ya faru ne awanni kadan bayan daruruwan masu zanga-zanga sun cinna wuta a ofishin jakadancin Sweden da ke Bagadaza yayin da birnin Stockholm ya sake bai wa wasu mutane izinin sake kona Alkur'ani mai tsarki.
Wasu bidiyoyi sun nuna masu zanga-zangar a ofishin jakadancin na Sweden suna daga tutoci da kwalaye masu dauke da hotunan fitaccen malamin mazahabin Shia Muqtada al Sadr.
A watan jiya, Sadr ya yi kira a yi zanga-zangar kyamar Sweden sannan a kori jakadanta da ke Iraki bayan wani mai zafin kin Musulunci ya kona Alkur'ani a Stockholm.
Bayana aukuwar wannan lamari, an bayar da sanarwar rufe ofishin jakadancin Sweden a Iraki ba tare da bayyana lokacin da za a sake bude shi ba.
Ma'aikatar harkokin wajen Sweden ta ce babu 'yan kasarta da suka jikkata sakamakon kona ofishin jakadancinsu.