Labarin rikicin Isra'ila da falasdinawa da ya wajaba a karanta / Design: Elif Cansin Senol

Daga Chloe Gill-Khan

Ana ci gaba da yin Allah wadai kan mayar da martanin wuce gona da iri da Isra'ila ke yi a Gaza bayan harin da Ƙungiyar Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoba. Duniya na kallon martanin a matsayin keta dokar jinƙan bil'adama ta Duniya.

Kawo yanzu, babu wani matsin lamba daga ƙasashen duniya da ya iya dakatar da aikata laifukan yaƙi da Isra'ila ke yi da kuma kashe farar-hula da ba su ji ba ba su gani ba sama da dubu tara a Gaza, waɗanda galibinsu mata da ƙananan yara ne.

"An katse hanyar sadarwa ta intanet da layukan waya a Gaza. Majalisar Dinkin Duniya da ƙasashe da yawa irin su Turkiyya, da Sifaniya, da Ireland, da Rasha da kuma Sin, dukkansu, sun yi kira da a tsagaita wuta nan-take, kuma Oxfam ta ce Isra'ila na amfani da yunwa a matsayin wani makamin yaƙi.

Antonio Guterres, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi wata magana da ta tabbata a tarihi, cewa, harin da Hamas ta kai "ba haka siddan ya faru ba".

Duk da Guterres ya jaddada cewa hakan bai halatta harin na Hamas ba, amma martanin Isra'ila ya zo da sauri, kuma a fayyace. Jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya, Gilan Erdan, ya yi kira ga Guterres ya yi marabus, sannan aka soke bizar tafiye-tafiye ta jami'an Majalisar Dinkin Duniya domin a koya mata hankali.

Wane irin hankali kenan wannan? Faɗar gaskiya a kan abin da tarihi ya tabbatar ya zama laifi, kuma dole sai an ɗauki hukunci a kansa? A ina muke rayuwa ne? A zamanin samar da bayanai ko kuma zamanin George Orwell na 1984.

Amma abu mafi muhimmanci shi ne, me hakan ke gaya mana game da asalin abin da ke faruwa?

Abin da ya fito fili shi ne tsammaninmu cewa intanet za ta zama kafa ƴar ba- ruwanmu, a matsayinta na kafar sadarwa. Haramcin, da labaran ƙarya da kuma nuna son rai, na ci gaba da yin babakere a kan gaskiyar abin da ke faruwa - a Gaza.

Domin maganin bazuwar ƙarairayi da shaci-faɗi da kuma son rai da ke zagayawa a kafafen watsa labarai da na intanet, na samar da litattafai da za su taimaka a fahimci abin da ke faruwa a Gaza, da yankunan Falasdinawa da aka mamaye da kuma Isra'ila.

Tsawon shekaru, na yi aiki a Shagon Sayar Da Litattafai na Al Saqi, wani Shagon litattafai da ya ƙware wajen samar da bayanai game da Gabas Ta Tsakiya, kuma na samu sahihan bayanai a kan wannan fagen.

Idan aka yi la'akari da ƙwarewata a fannin tarihi da adabi, nazari a kan mulkin mallaka da na bayan mulki mallaka, na yi imanin cewa, akwai buƙatar gaggawa fiye da kowane lokaci, da mu samar wa kanmu makami mafi ƙarfi, da za mu iya samu - Ilimi.

Na samar da jerin littattafai domin gabatar da muhimman tunani.

Harshe da yadda muka fahimci Falasdinu da Isra'ila: (baƙi) mulkin mallaka, kisan ƙare-dangi da nuna wariyar launin fata.

Language and how we understand Palestine and Israel: (settler) colonialism, ethnic cleansing and apartheid. Design: Elif Cansin Senol  

Gomman shekaru, an yi amfani da lafuza kamar rikicin Larabawa da Isra'ilawa, abin da ya dasa ɗambar yadda aka fahimci lamarin. Kwarmata bayanan da ya kamata a killace, da aikace-aikace da suka biyo baya, ya ƙalubalanci labaran da aka fi yarda da su:

The Hundred Years’ War on Palestine: A History of Settler Colonial Conquest and Resistance, Rashid Khalidi, 2020

The Ethnic Cleansing of Palestine, Ilan Pappe, 2007

Israeli Apartheid: A Beginner’s Guide, Ben White, 2014

Dalilai na Aƙidu: Siyasar aƙidar kafa ƙasar Yahudawa ta asali, Aƙidar Kirista masu goyon bayan kafa ƙasar Yahudawa da kuma Masu tsattsauran ra'ayin na Yahudawa.

Dalilai na Aƙidu: Siyasar aƙidar kafa ƙasar Yahudawa ta asali, Aƙidar Kirista masu goyon bayan kafa ƙasar Yahudawa da kuma Masu tsattsauran ra'ayin na Yahudawa.

Siyasar aƙidar kafa ƙasar Yahudawa ta asali, wacce ta bayyana a ƙasashe a ƙarni na goma sha tara, ta duƙufa wajen kafa ƙasar Yahudawa ta asali a ƙasar Falasdinu.

Domin karatu sosai game da gabatarwar batutuwan siyasar Masarautar Biritaniya, da yaƙin Duniya na Biyu, Da Aƙidar Kafa Ƙasar Yahudawa da kuma Palastinu, ga wannan:

Legacy of Empire: Britain, Zionism and the Creation of Israel, Gardner Thompson, 2019

Har ila yau, ka duba babina a kan yaƙi tsakanin Birtaniyya da Turai. Ya tattauna a kan matsalolin siyasa na lokacin da kuma gazawa Majalisar Dinkin Duniya ta da (League of Nations) da kuma magajiyarta ta yanzu (United Nations) na hana faruwar bala'i irin na Yaƙin Duniya Na Biyu, saboda ƙasashe sun taka doka. Waɗannan batutuwan suna da alaƙa kai tsaye a kan halayya wajen samar da ƙasar Yahudawa ta asali a cikin ƙasar Palasdinu:

"Nahiya Mai Duhu: marasa rinjaye, jinsi da kuma doka a Turai," a siyasar haɗewar jama'a : Doka,Jinsi da Adabi a Birtaniyya da Faransa bayan yaƙi, Chloe Gill-Khan, 2018,shafi na 36-66.

Yana da muhimmanci a bambance tsakanin siyasar Aƙidar kafa ƙasar Yahudawa ta asali daga yadda wasu Yahudawa masu kishin addini suka ɗauki Falasdinu a matsayin wajen ziyarar ibada mai tsarki, ba inda zai iya zama ƙasar Yahudawa ba. Galibin Yahudawa masu ra'ayin mazan jiya suna adawa da aƙidar kafa ƙasar Yahudawa.

Like Birds in a Cage: Christian Zionism’s Collusion in Israel’s Oppression of the Palestinian People, David M. Crump, 2021

Littafin Crump da ya fayyace gaskiya ya bayyana ƙin amincewarsa da aƙidar Kirista masu goyon bayan kafa ƙasar Yahudawa da ya taso a cikinta.

Ya bayyana yadda Kirista masu aƙidar goyon bayan kafa ƙasar Yahudawa suka yi imanin cewa Falasdinu wani cikar alƙawari Baibul ne ga Yahudawa, amma suka rintse ido game da cin zalin Falasdinawa da Isra'ila ke yi, suna narka dukiya wajen ganin Isra'ila ta ci gaba da riƙe madafun iko:

"Ɓangare mai goyon bayan Isra'ila mafi girma da ƙarfin faɗa a ji Amurka shi ne Cocin Evangelical (Crump, 2021:38)."

Har wa yau a karanta:

Christian Zionism: Road-Map to Armageddon?, Stephen Sizer, 2021

Da:

The Origins of Christian Zionism: Lord Shaftesbury and Evangelical Support for a Jewish Homeland, Donald M. Lewis, 2014

Jewish Fundamentalism in Israel: Second Edition, Israel Shahak and Norton Mezvinsky, 2004

Wannan ingantaccen littafin ya yi nazarin tarihi da cigaban masu tsattsauran ra'ayin addinin Yahudanci da kuma mummunan tasirin da suke da shi a kan siyasar Isra'ila.

Ƴan Isra'ila da Yahudawa masu adawa da kafa ƙasar Yahudawa ta asali.

Ƴan Isra'ila da yahudawa masu adawa da kafa ƙasar Yahudawa ta asali. / Design: Elif Cansin Senol

The Making and Unmaking of a Zionist: A Personal and Political Journey, Antony Lerman, 2012

Wrestling with Zionism: Jewish Voices of Dissent, Daphna Levit, 2020

The Myths of Liberal Zionism, Yitzhak Laor, 2017

Tarihi da Falasdinu bayan 1948 da kuma Rayuwar Falasdinawa

Tarihi da Falasdinu bayan 1948 da kuma Rayuwar Falasdinawa / Design: Elif Cansin Senol  

Palestine: A Four Thousand Year History, Nur Masalha, 2022

On Palestine, Noam Chomsky and Ilan Pappe, 2015

A History of Modern Palestine, Ilan Pappe, 2022

The Biggest Prison on Earth: A History of the Occupied Territories, Ilan Pappe, 2017

Gaza: An Inquest into its Martyrdom, Norman Finkelstein, 2021

Gaza in Crisis: Reflections of Israel’s War Against the Palestinians, Ilan Pappe and Noam Chomsky, 2011

The Forgotten Palestinians: A History of the Palestinians in Israel, Ilan Pappe, 2013

Doka

Justice For Some: Law and the Question of Palestine, Noura Erakat, 2019

A History of False Hope: Investigative Commissions in Palestine, Lori Allen, 2020

Lanƙwasa Harshe, aƙidar ƙin jinin Yahudawa:

Beyond Chutzpah: On the Misuse of Anti-Semitism and the Abuse of History, Norman G. Finkelstein, 2008

‘Jewish settlers stole my house. It’s not my fault they’re Jewish’, Mohammed El-Kurd, 2023 (essay)

The Holocaust Industry: Reflections on the Exploitation of Jewish Suffering, Norman G Finkelstein, 2015

Adabi, Al'ada da Fasaha

Adabi, Al'ada da Fasaha / Design: Elif Cansin Senol

Akwai Adabin Falasdinawa masu yawa. Waɗannan da ke tafe zaɓaɓɓun shawarwari ne:

The Butterfly’s Burden, Mahmoud Darwish, 2007

Palestinian Walks: Notes on a Vanishing Landscape, Raja Shehadeh, 2008

I Was Born There, I Was Born Here, Mourid Barghouti, 2012

Mornings in Jenin, Susan Abulhawa, 2010

Nabil Anani: Palestine, Land and People, Anani, 2018 (beautiful artworks of Anani).

Dr Chloe Gill-Khan mai bincike ce ta musamman kuma marubuciya. Ta kwashe shekaru da dama tana aiki a matsayin malamar jami'a, kuma ta rubuta littafi kan siyasar Birtaniya da Faransa; The Politics of Integration: Law, Race and Literature in Post-war Britain and France, 2017.

TRT World