Aƙalla mutane 65 ne suka bace bayan zaftarewar kasa ta afka da wasu motocin bas na fasinja guda biyu a kasar Nepal ranar Juma'a.
Ifti'la'in ya faru ne a gundumar Chitwan mai tazarar kilomita 86 daga yankin yamma da babban birnin kasar Kathmandu, a daidai lokacin da zaftarewar kasa ta nutse da motocin bas din cikin kogin Trishuli.
Indradev Yadav, babban jami'in gundumar Chitwan, ya ce haɗarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na safe (2145GMT, Alhamis), kamar yadda jaridar Kathmandu Post ta ruwaito.
Ɗaya daga cikin motocin bas din dake ɗauke da mutane 41 ya taso ne daga Kathmandu zuwa Gaur yayin da dayan da ke ɗauke da fasinjoji 24 ke kan hanyarsa daga Birgunj zuwa Kathmandu.
A shekarun baya-bayan nan ƙasar Nepal ta fuskanci ifti'la'i da dama.
Mutum uku daga cikin fasinjojin da ke cikin motar bas ɗin da ke tafiya zuwa Gaur sun yi nasarar kuɓuta da ransu ta hanyar tsalle daga cikin motar.
Chitwan na daya daga cikin gundumomi 77 na ƙasar Nepal wanda ke yankin kudu maso yammacin lardin Bagmati.