Akalla mutane 14 ne suka mutu yayin da 102 - ciki har da jami'an soji 22 - suka bace a arewa maso gabashin Indiya bayan da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya yi sanadin fashewar wani tafkin kankara, wanda ya janyo ambaliya a wani kududdufi.
Iftila'in, wanda ya shafi kusan mutum 22,000, ya kasance mafi a jerin barnar da aka taba samu a yankin tsaunukan kudancin Asiya da ke da alaka da sauyin yanayi mai tsanani.
"Aikin ceto na gudana ne ba kakkautawa cikin yanayin damina kuma cikin ruwan da ke kwarara ta kogin Teesta da kan hanyoyi da gadoji wadanda tuni ruwan ya shafe su," a cewar mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Indiya a ranar Alhamis ta shafin X, wanda aka fi sani da Twitter.
An sheka ruwan sama mai yawa cikin kankanin lokaci a tafkin Lhonak a ranar Laraba, wanda ya haifar da ambaliyar ruwa a tsibirin Teesta, mai tazarar kilomita 150 daga arewacin Gangtok, babban birnin jihar Sikkim, kusa da kan iyakar China.
Hukumar kula da bala’o’i ta jihar ta ce mutane 26 ne suka jikkata, yayin da wasu 102 kuma suka bace, ya zuwa safiyar ranar Alhamis.
Kazalika gadoji goma sha daya ne ruwan ya yi awon gaba da su.
Hotuna da bidiyoyin da kamfanin dillancin labarai na ANI ya fitar sun nuna yadda ruwan ya mamaye wasu gine-gine inda gidaje da dama suka ruguje yayin da sansanonin sojoji da sauran kayayyakin aiki suka lalace sannan ababen hawa da dama sun nutse.
Hukumar kula da yanayi ta yi gargadi kan yiwuwar zabtarewar kasa da kuma katsewar zirga-zirgar jiragen sama yayin da ake sa ran karin ruwan sama a cikin kwanaki biyu masu zuwa a wasu sassan Sikkim da makwabtan jihohin kasar.
Sauran yankunan da ke da tsaunuka a Indiya da Pakistan da Nepal da ke makwabtaka da juna, sun fuskanci ruwan sama kamar da bakin kwarya da ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa a 'yan watannin nan, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
A bara ne Pakistan ta dora alhakin matsalar ambaliya kan sauyin yanayi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi sakamakon ruwan sama da ya yi sanadin lalata tituna da amfanin gona da kuma kayayyakin more rayuwa da gadoji tare da kashe akalla mutane 1,000.
"Abin takaici ne sosai, wannan ne yanayi mafi mufi na baya-bayan nan cikin jerin ambaliyar ruwa da yankin Hindu Kush-Himalayan ya taba fuskanta a lokacin damina, lamarin da ya nuni raunin da yankin ke fama da shi ga sauyin yanayi." a cewar babban darektan cibiyar kasar Nepal kan inganta Hadin gwiwar yankunan tsaunuka Pema Gyamrsho.