1420 GMT — Firaministan Birtaniya ya yi kira da a yi gaggawar tsagaita wuta a Gaza
Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza a lokacin da yake jawabi a majalisar dokokin kasar, inda ya jaddada bukatar kai agajin gaggawa da kuma mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su.
"Na yi magana da shugabannin Isra'ila da hukumar Falasdinu," in ji Starmer. "Na bayyana a fili cewa ina goyon bayan 'yancin Isra'ila na samun tsaro da kuma bukatar ganin an dawo da mutanen da aka yi garkuwa da su.
"Sannan kuma na bayyana karara cewa ba za a yarda da halin da ake ciki a Gaza ba, kuma duniya ba za ta ɗauke idonta daga halin da fararen hula da ba su da laifi ke ciki ba a Gaza, da suka haɗa da mata da yara, waɗanda ke ci gaba da fuskantar kisa da cututtuka, da ƙaura."
"Ba za a tafi a haka ba. Muna bukatar tsagaita wuta nan take: a saki wadanda aka yi garkuwa da su, a kai agaji, ina nufin gagarumin ƙarin taimakon jinƙai. Wannan ita ce manufar wannan gwamnati," in ji shi.
1154 GMT — Rundunar Sojin Isra’ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 23 a wasu sabbin hare-hare da ta kai Gaza, wanda hakan ya kawo adadin Falasɗinawan da ta kashe a Gaza zuwa 39,006 tun daga 7 ga watan Oktoba, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta tabbatar.
Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ƙara da cewa akwai wasu 89,818 waɗanda suka jikkata sakamakon hare-haren na Isra’ila.
Ma’aikatar Lafiyar ta Gaza ta bayyana cewa akwai jama’a da dama waɗanda har yanzu suna nan ƙarƙashin ɓaraguzai bayan gini ya faɗo masu sakamakon hare-haren na Isra’ila
1132 GMT — Jamus 'ba ta goyon bayan mamayar Isra'ila': Ma'aikata
Jamus ta ce "ba ta goyon bayan manufofin mamayar Isra'ila" bayan da kotun Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da 'yancin cin gashin kai ga Falasdinawa tare da yanke hukuncin cewa dole ne a kwashe matsugunan Yahudawa ba bisa ka'ida ba a yankunan da ta mamaye.
Yayin da Jamus ke goyon bayan Isra'ila saboda tarihin da ke da alhakin da ya rataya a wuyanta ga kasar Isra'ila ba ya nufin "tana goyon bayan manufofin mamayar Isra'ila," in ji mataimakin kakakin ma'aikatar harkokin wajen Christian Wagner ga manema labarai a Berlin.
Ya kara da cewa "da farko ya rage ga gwamnatin Isra'ila ta yanke shawara daga wannan rahoton (kotun Majalisar Dinkin Duniya).