Firaiministan da gwamnatin Chadi ta naɗa ya fito takarar shugaban ƙasa

Firaiministan da gwamnatin Chadi ta naɗa ya fito takarar shugaban ƙasa

Firaiministan da gwamnatin Chadi ta naɗa Succes Masra ya bayyana aniyarsa ta takarar shugaban ƙasa
A ranar 10 ga watan Maris 2024 ne Succes Masra ya ƙaddamar da shirinsa na neman takarar shugaban ƙaas. / Hoto: AFP

Firaiministan Chadi ta gwamnatin soja naɗa ya bayyana cewa zai yi takarar shugaban kasar a zaɓen da za a yi ranar 6 ga watan Mayu, ƴan kwanaki bayan shugaba mai ci, Janar Mahamat Idriss Deby Itno ya bayyana cewa zai tsaya takara.

Succes Masra, wanda tsohon jagoran hamayya ne, ya dawo daga gudun hijira ne ya kuma sanya hanya kan yarjejeniyar sasantawa da Deby Itno kafin ya zama firimiya a bana.

Ƴan hamayyar sun ce takarar Masra wani shiri ne kawai don nuna cewa an yi gwagwarmaya a zaɓen da aka tabbatar jagoran gwamnati ne zai lashe.

Masra, mai shekara 40 ya bayyana aniyarsa ta yin takara ne a wajen wani gangamin siyasa da ɗaruruwan magoya bayan jam'iyyarsa ta Transformation Party suka halarta ranar Lahadi, yana cewa yana so ya "warkar da zuciya ya haɗa kan mutane."

'Yarjejeniyar Jarumta'

Da yake mayar da martani kan masu sukarsa da suka yi watsi da matakin nasa cewa duk bakinsu ɗaya da shugaban gwamnati, Masra ya kare "yarjejeniyar ta jarumta" a matsayin wacce ke nufin "fafutukar da muke yi ta neman adalci har abada ba za ta taɓa zama fafutukar ramuwar gayya ba."

Masra ya bar aikinsa ne a Bankin Bunƙasa Ci Gaban Afrirka a shekarar 2016 ya kafa jam'iyyar Transformers.

Ya kasance ɗaya daga manyan masu hamayya da tsohon shugaban Chadi, Field Marshal Idrss Deby Itno, mahaifin shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya, wanda ya mutu a 2021 bayan shafe shekara 30 yana mulki.

Masra ya kuma yi tir da "juyin mulkin" da ya bai wa Deby ƙarami damar ɗarewa kan kujera ba tare da ɓata lokaci ba, bayan akwai janar-janar 15 a gabansa.

Yarjejeniyar sasantawa

Masra ya gudu daga Chadi kafin ya koma ƙasar ranar uku ga watan Nuwamba inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar sasantawa da ta yafewa waɗanda suka yi zanga-zangar ranar 22 ga watan Oktoba, da kuma waɗanda suka buɗe wuta.

Yunƙurinsa na neman shugabanci wani "wasan kwaikwayo ne, takara ce ta bogi don raka shugaban mulkin soja yin ta-zarce," a cewar Max Kemkoye, mai magana da yawun gamayyar jam'iyyun hamayyya ta GCAP a hirarsa da AFP.