Ɗaure tsohon firaiministan ƙasar Imran Khan ya jawo fargaba matuƙa a ƙasar. / Hoto: AFP

Aƙalla mutum biyu aka kashe a wasu hare-haren bam biyu da aka kai a wajen wasu ofisoshin zaɓe a kudu maso yammacin Pakistan, kamar yadda hukumomi da kafafen watsa labarai na kasar suka tabbatar a jajibirin zaɓen ƙasar wanda ke tattare da rikici da ce-ce-ku-ce.

Harin da aka kai na farko ya faru ne a kusa da ofishin wani ɗan takara mai zaman kansa a gundumar Quetta, wanda ke da nisan kilomita 50 daga birnin Quetta, da kuma kilomita 100 daga iyakar ƙasar daga Afghanistan.

Muƙaddashin ministan watsa labarai na lardin Balochistan Jan Achakzai da ƴan sandan Quetta duka sun ce adadin waɗanda suka rasu sakamakon tashin bam ɗin ya kai 14, inda sama da 30 suka samu rauni.

Tashin bam ɗin na biyu ya faru ne a kusa da ofishin wani ɗan takara na Jam’iyar Jamiat Ulema-e-Islam-F (JUI-F) a birnin Killa Saifullah – mai nisan kilomita 120 daga gabashin ƙasar.

Mataimakin kwamishina na birnin Yasir Bazai ya shaida cewa mutum 12 rasu sakamakon tashin bam ɗin, wanda ya faru a wajen ofishin JUI-F.

A watan Yulin bara, mutum 44 sun rasu sakamakon harin ƙunar-baƙin-wake a wani taron siyasa a arewa maso yammacin lardin Khyber Pakhtunkhwa.

Sama da mutum dubu ɗari biyar aka soma turawa a ranar Laraba a jajibirin zaɓen, inda hukumomin ke rarraba takardun jefa ƙuri’a ga sama da rumfuna zaɓe 90,000.

Ana cikin fargaba a zaɓen da ke tafe bayan tura tsohon firaiministan ƙasar Imran Khan gidan yari, wanda shi ne ya lashe zaɓen ƙasar a 2018, sai dai majalisa ta hamɓarar da gwamnatinsa bayan wata ƙuri’ar yanke ƙauna.

TRT World